Aisha Buhari hazikar dalibata ce a darasin Physics, Malamar uwargidan shugaban kasa
- Tsohuwar malamar makaranta kuma kwamishinan ilimi a halin yanzu, Mrs Wilbina Jackson ta ce ta karantar da uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari
- Kamar yadda Mrs Jackson ta bayyana, Aisha Buhari daliba ce mai hazaka a yayin da ta karantar da ita Physics a makarantar sakanadren Yelwa da ke Adamawa
- Malamar ta yi kira ga iyaye kan cewa ilimantar da 'ya'ya mata ba asara bane kamar yadda wasu ke ganin cewa aure daga baya diya mace za ta yi, ta koma kasan wani
Tsohuwar malamar makaranta kuma kwamishinar ilimi ta jihar Taraba, Mrs. Wilbina Jackson, ta kwatanta matar shugaban kasan Najeriya, Aisha Buhari, a matsayin daya daga cikin hazikan daliban darasinta na Physics a makarantar sakandaren Yelwa, inda ta koyar shekaru masu yawa da suka gabata.
Malamar tsohuwar dalibar jami'ar Ahamdu Bello ce da ke Zaria kuma ta kammala digirinta a fannin Physics a shekarar 1983.
The Sunnews ta ruwaito cewa, ta sanar da hakan ne yayin da ta ke bayanin yadda jihar Adamawa ta kasance jihar da ta dade ta na bai wa yara mata damar karatu kamar yadda ta ke bai wa yara maza.
A yayin zantawa da manema labarai a Kaduna yayintaron kaddamar da National Gender Education Policy in Northern Nigeria wanda aka yi a wani otal a Kaduna, kwamishinan ta kara da cewa Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya bayar da himma wurin tabbatar da an gaggauta tabbatar da sabbin dokokin a jihar, Sunnews ta ruwaito.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kamar yadda tace, "A jihar Adamawa, ba mu da matsalar kebance jinsi wurin karatu saboda yara mata da maza duk daya suke. Kamar yadda ku ka ganni a matsayin kwamishina, hakan na nuna cewa mata na zuwa makaranta a jihar.
"Na karanci Physics a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria kuma na kammala a shekarar 1983. Tuntuni na ke koyar da darasin a Adamawa. Na koyar da mata da maza masu tarin yawa.
"A bangaren kasafin ilimi a jihar, ba mu ware ilimin mata ko na maza, gwamnan ya na kokari.
“Cike da alfahari zan iya sanar da 'yan Najeriya cewa, ni malamar uwargidan shugaban kasa ce, Aisha Buhari. Ni na koyar da ita darasin Physics kuma tana daya daga cikin dalibai na masu hazaka. Babu shakka za ta iya tuna Mrs Jackson a makarantar sakandaren Yelwa amma ba zan iya tuna shekarar da ta kare ba.
“Toh in har mace kamar wannan za ta iya fitowa daga Adamawa, hakan na nufin cewa jihar na kokarin ilimantar da 'ya'yansu ba tare da duban jinsi ba.
“A lokaci na, wasu iyayen na cewa ba za su bata kudinsu ba kan mace da za ta zama matar aure a gaba, karkashin wani namiji. Amma yanzu da na zama kwamishina, iyaye su san cewa ilimantar da 'ya'ya mata ba asarar kudi bane," tace.
Aisha Buhari, BUA, Indimi da Gambari za su samu kyautar digirin Dakta daga jami’ar Arewa
A wani labari na daban, mai dakin shugaban Najeriya, Aisha Muhammadu Buhari da Farfesa Ibrahim Gambari su na cikin wadanda za su samu karramawa da digirin dakta.
Jaridar Punch ta ce jami’ar jihar Kwara da ke garin Malete za ta karrama uwar gidar shugaban kasa, Aisha Muhammadu Buhari da digir-digir watau dakta.
Haka zalika shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari zai samu irin wannan karramawa a wajen bikin yaye daliban da za ayi.
Asali: Legit.ng