Hukumar NHRC zata binciki mummunan kisan da akai wa Fulani a jihar Edo
- Hukumar kare hakkin bil adama ta ƙasa (NHRC) ta sha alwashin gudanar da bincike kan kisan Fulani a jihar Edo
- Sakataren hukumar, Tony Ojukwu, yace lamarin ya munana sosai, kuma duk me hannu a kisan zai girbi abinda ya shuka
- Kungiyar matasan Fulani ta kasa (AMFN) ta ziyarci hukumar NHRC, inda suka shigar da korafi kan wasu yankuna a Edo da Anambra
Abuja - Hukumar kare hakkin ɗan adam ta ƙasa (NHRC) a ranar Litinin tace zata gudanar da bincike kan zargin kashe wasu Fulani 4 a jihar Edo.
Punch ta ruwaito cewa ana zargin wasu yan bijilanti da kuma matasan yanki da kashe Fulanin ba tare da wani dalili ba.
A cewar hukumar, ya zama wajibi ta yi bincike domin waɗan da suka aikata aika-aikan su girbi abinda suka shuka, kuma ya zama izina ga yan baya.
Mataimakin daraktan yaɗa labarai na hukumar, Hajiya Fatima Mohammed Agwai, ita ce ta bayyana haka a wata sanarwa da ta fitar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sanarwan tace Sakataren NHRC, Tony Ojukwu, shine ya bada wannan tabbacin yayin da mambobin kungiyar matasan Fulani ta ƙasa suka ziyarce shi.
Matasan Fulanin sun ziyarci hukumar ne domin shigar da korafi kan kisan yan uwansu da akayi a Edo, da harin da ake kaiwa mambobinsu a Anambra.
Wane mataki NHRC zata fara ɗauka?
Ojukwu ya ƙara da cewa hukumar zata tuntuɓi ofishin sufeta janar na yan sanda (IGP) da kwamishinan yan sanda na jihar Edo, domin samun ainihin bayanin abinda ya faru.
Yace:
"Kisan gillan da akaiwa Fulani shine mafi muni kuma makurar abin takaici domin babu wanda ke da damar ɗaukar rayuwar wani, kowaye shi a cikin al'umma."
"Kotu ce kaɗai take da dama da ikon yanke wa wani wanda ta kama da laifi, hukuncin kisa."
Yace kowane ɗan Najeriya yana da rigar kariya da doka ta bashi ba tare da duba addininsa ko ƙabilar da ya hito daga ciki ba.
Meya kai kungiyar fulani NHRC?
Shugaban kungiyar AMFN, Alhaji Shuaibu Haruna Sogiji, yace sun kai ziyara hukumar NHRC ne domin, "Shigar da korafi kan wasu yankuna a kudancin Najeriya."
Sogiji ya koka sosai kan kisan gilla da kuma ƙone wasu Fulani hudu har Lahira a wani ƙauyen jihar Edo, yayin da suka je siyan kayan abinci.
Ya kuma tabbatar da cewa sun shigar da kara gaban shugaban ofishin yan sanda (DPO) na kauyen da lamarin ya faru a Edo, "Amma babu wani mataki da aka ɗauka," domin shawo kan lamarin.
A wani labarin na daban kuma Rikici ya barke, yan Acaba sun lakadawa yan sanda dukan tsiya a Legas
Hukumar yan sanda ta gurfanar da wasu yan acaba a gaban kotun majistire bisa zargin lakaɗawa jami'anta duka da kuma lalata motocin sintiri.
Ɗan sanda mai gabatar da ƙara, ya shaida wa kotun cewa yan acaban da sauran abokan aikinsu sun bar yan sanda biyu da jinya a Asibiti.
Asali: Legit.ng