Da Dumi-Dumi: Jami'an DSS sun damke shugaban hukumar CPC, Janar Dambazau a Kano

Da Dumi-Dumi: Jami'an DSS sun damke shugaban hukumar CPC, Janar Dambazau a Kano

  • Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta kama shugaban hukumar CPC reshen jihar Ƙano, Janar Idris Dambazau
  • Rahotanni sun bayyana cewa jami'an DSS sun kame Dambazau ne bisa zargin ɓarnatar da tattalin arzikin kasa
  • Wata majiya tace Dambazau ya kulle wasu gidajen man fetur a jihar, ba tare da bin ka"idoji da dokokin kundin mulki ba

Kano - Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta yi ram da shugaban hukumar Consumer Protection Council (CPC) na jihar Kano, Janar Idris Dambazau, bisa zargin yiwa tattalin arziki zagon ƙasa.

A rahoton Vanguard, wata majiya dake kusa da jami'an tsaro tace, DSS na zargin Janar Dambazau da garƙame gidajen man fetur 7, ba tare da bin ƙa'ida ba.

Haka nan kuma majiyar ta ƙara da cewa an yi kokarin sa Janar Danbazau ya buɗe waɗan nan gidajen man fetur amma ya yi kunnen uwar shegu da zancen.

Kara karanta wannan

Kannywood: Dalilin da yasa aka cire Salma diyar tsohon gwamna a shirin Kwana Casa'in

Jami'an DSS
Da Dumi-Dumi: Jami'an DSS sun damke shugaban hukumar CPC, Janar Dambazau a Kano Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Dambazau ya yi haka duk da sanin cewa yana kokarin yi wa doka hawan ƙawara ne, wanda abinda ya yi ya zarce karfin ikon ofishin da yake rike da shi.

Majiyar tace:

"Jami'an tsaro na ganin abinda Dambazau ya yi a matsayin ɓarnatar da tattalin arziki, tare da nufin jawo matsalar karancin kayayyaki a jihar Kano, bayan kuma akwai su."

Laifin da Dambazau ya aikata

Majiya daga cikin hukumar DSS, wanda ya nemi a sakaya bayanansa, yace sashi na 48 na kundin mulkin Najeriya, ya bayyana cewa duk wata ma'aikata ko hukumar gwamnaati da zafa ɗauki wani mataki da zai tasiri a ɓangaren samar da man fetur, to wajibi ne ya nemi shawara.

Sashin ya kuma bayyana cewa neman shawarin zai zo a farko kafin zartar da doka ko umarni, wanda a cewar majiyar Dambazau ya yi faatali da shi.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Iyayen Ango da Yan uwansa sun mutu awanni kadan bayan kammala daura Aure

Hakanan kuma DSS tace ko bayan neman shawarin masu ruwa da tsaki, sai wannan hukuma ta yi nazari kan shawarwarin, kuma ta sanar da matakin da ta ɗauka kafin zartarwa.

Dailytrust ta ruwaito cewa za'a gurfanar da shi a gaban kotu ranar Litinin 6 ga watan nuwamba.

A wani labarin na daban kuma Rikici ya barke, yan Acaba sun lakadawa yan sanda dukan tsiya a Legas

Hukumar yan sanda ta gurfanar da wasu yan acaba a gaban kotun majistire bisa zargin lakaɗawa jami'anta duka da kuma lalata motocin sintiri.

Ɗan sanda mai gabatar da ƙara, ya shaida wa kotun cewa yan acaban da sauran abokan aikinsu sun bar yan sanda biyu da jinya a Asibiti.

Asali: Legit.ng

Online view pixel