Fashewar bama-bamai a Maiduguri: Rundunar soji ta magantu, ta ce a kwantar da hankali

Fashewar bama-bamai a Maiduguri: Rundunar soji ta magantu, ta ce a kwantar da hankali

  • Rundunar sojin Najeriya ta magantu bayan da aka samu fashewar bama-bamai a wasu yankunan Maiduguri
  • Rahotanni sun ce, an ji fashewar rokoki da wasu unguwanni a Maiduguri, lamarin da ya haifar da zaman dar-dar ga mazauna
  • Rundunar soji ta ce kowa ya kwantar da hankali, rundunoni na aiki don tabbatar da tsaro da kuma fatattakar 'yan ta'adda

Borno - Rundunar sojin Najeriya a ranar Asabar ta kawar da fargabar mazauna Maiduguri, biyo bayan fashe-fashen da suka faru a wasu al’ummomi a babban birnin na jihar Borno, Daily Trust ta ruwaito.

Rahotanni sun bayyana yadda karar fashewar wasu abubuwa a unguwar Gomari da jerangiyar gidaje na 1000 a Maiduguri da sanyin safiyar Asabar ta haifar da tashin hankali.

Kara karanta wannan

Sojoji sun sheke dan IPOB yayin da tsagerun ke kokarin sace likitoci a jihar Imo

Da take mayar da martani kan lamarin, rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da cewa wasu 'yan ta'adda na Boko Haram ne da kuma 'yan kungiyar ISWAP suka yi ta harbe-harbe a cikin wadannan yankuna.

Wurin da aka samu fashewa a Maiduguri
Fashewar bama-bamai a Maiduguri: Rundunar soji ta magantu, ta a kwantar da hankali | Vanguard
Asali: Facebook

A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, Brig.-Gen. Onyema Nwachukwu ya fitar, ya ce ‘yan ta’addan sun yi yunkurin yin amfani da fashe-fashen ne wajen kwace birnin Maiduguri.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Nwachukwu ya ce dakarun rundunar hadin gwiwa ta JTF a arewa maso gabas, Operation Hadin Kai suna daukar mataki dangane da tabarbarewar tsaro, inda ya baiwa mazauna garin tabbacin kada su firgita.

A cewarsa:

“Wannan mummunan lamari ya haifar da barna da fargaba a yankunan. Ko da yake, ba a rasa rai ba, abin bakin cikin shine an samu karamin rauni."

Kakakin Rundunar ya ce sojojin kasa tare da hadin gwiwar rundunar sojin sama na OPHK sun mayar da martani cikin gaggawa tare da mamaye yankin ta sama da kasa wanda ya yi nasarar kawar da barazanar da kuma yunkurin kutsawar 'yan ta'addan.

Kara karanta wannan

Jami’an tsaro sun kama matar da ta rufe ‘yar shekara 6 a daki na wata da watanni

Ya kara da cewa:

"An kuma umarci mutanen Maiduguri da su ci gaba da gudanar da harkokinsu na zamantakewa da tattalin arziki tare da bayar da bayanai da suka dace kan motsin wadannan miyagun mutane."

Hukumar jiragen sama ta musanta rahotannin tashin bam a filin jirgin Maiduguri

Hukumar kula da filayen tashi da saukar jiragen sama ta Najeriya (FAAN) ta musanta rahotannin tashin bam a filin jirgin Maiduguri, inji rahoton Premium Times.

Wata sanarwa a ranar Asabar da kakakin FAAN, Henrietta Yakubu ya fitar, ta ce:

"Ba a kai wa filin jirgin saman hari ba, kuma ba a kai hari ko wanne bangarensa ba."

Sanarwar ta kara da cewa:

"Game da rahoton da aka samu ta yanar gizo da ke cewa bam ya tashi a filin jirgi na Maiduguri da ake zargin mayakan Boko Haram ne suka shirya, hukumar ta FAAN ta sanar da fasinjoji da sauran jama'a cewa babu wani fashewa, ko kutse a filin jirgin Maiduguri."

Kara karanta wannan

'Yan banga sun jawo 'yan bindiga sun hallaka mazauna a Sokoto, gwamnati ta fusata

Mutane sun jikkata, yayinda ake harba manyan rokoki cikin garin Maiduguri

A wani bangaren, mazaunan rukunin gidajen 1000 Housing Estate dake cikin Maiduguri sun waye gari ranar Asabar da tashin bama-bamai.

Vanguard ta ruwaito cewa akalla karar bama-bamai hudu aka ji cikin gundumar Gomari da 1000 Housing Estate.

Ana kyautata zaton cewa yan ta'addan Boko Haram suka kai wannan hari ta hanyar harba rokoki cikin gari yayinda Sojoji ke kokarin kawar da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel