Jerin Abubuwa 5 da Kotu ta umurci DSS ta baiwa Nnamdi Kanu na walwala

Jerin Abubuwa 5 da Kotu ta umurci DSS ta baiwa Nnamdi Kanu na walwala

A ranar Alhamis, kotu ta cigaba da zaman kan shari'ar Shugaban kungiyar masu neman kafa kasar Biyafara, Nnamdi Kanu.

Zaman wanda ke gudana gaban Alkali Binta Nyako na babban kotun tarayya dake Abuja ta amsa bukatun lauyoyin Kanu.

Wannan karon an lura cewa babu jami'an tsaro a harabar kotun kuma hukumar DSS bata kawo Nnamdi Kani kotun ba.

Lauyan Kanu, Aloy Ejimakor ya bayyanawa SaharaReporters cewa kotun ta amsa bukatun da suka gabatar gaban kotun bisa halin da yake ciki a tsare.

Jerin Abubuwa 5 da Kotu ta umurci DSS
Jerin Abubuwa 5 da Kotu ta umurci DSS ta baiwa Nnamdi Kanu na walwala

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa:

"A karshe, Kotu ta yanke cewa zata saurari dukkan bukatunmu a zama na gaba kuma ta bada wadannan umurni:

1. A baiwa Mazi Nnamdu Kanu walwalan da yake bukata a tsare

2. A baiwa Kanu damar canza riga

3. A bari Kanu yayi ibadun addininsa na yahudanci

4. DSS ta bari Kanu ya karbi duk bakon da yake so

5. A bari Nnamdi Kanu yayi hulda da sauran fursunoni dake wajen

A riwayar TVC, sauran umurnin sune:

6. A yi dubi cikin kyawun abincin da yake ci

7. A bar shi ya ga Likita

A karshe, Lauyan Kanu ya kara da cewa kotun ta dage zama na gaba zuwa ranar 18 ga Junairu, 2022.

Yace:

"Bayan nazari cikin ayyukanta, kotun ta dawo da ranar zama na gaba zuwa 18 ga Junairu, daga 19 ga Junairu, 2022."

Asali: Legit.ng

Online view pixel