'Yan Sanda Sun Kama Mutumin Da Ya Shafawa Mata 14 Cutar Ƙanjamau a Legas

'Yan Sanda Sun Kama Mutumin Da Ya Shafawa Mata 14 Cutar Ƙanjamau a Legas

  • Yan sanda sun kama wani mutum da ya shafawa matarsa da wasu mata fiye da 12 cutar kanjamau
  • An kama Bolaniran Orimolade ne bayan wata kungiya mai kare hakkin yara da marasa galihu ta yi kararsa wurin yan sanda
  • Orimolade ya kasance yana karyar cewa shi shugaban tasha ne a kungiyar NURTW amma kungiyar ta nesanta kanta daga gareshi

Yan sanda sun kama wani Bolaniran Orimolade, mutumin da ya shafawa matarsa da yar ta da wasu mata da dama cuta mai karya garkuwar jiki ta HIV/AIDS a jihar Legas, SaharaReporters ta ruwaito.

Ebenezer Omejalile, babban jami'in kungiyar kare hakkin yara da mutane marasa galihu ta Advocates for Children and Vulnerable Peoples Network ne ya sanar da hakan.

Yan sandan Nigeria.
Yan Sandan Nigeria. Hoto: The Punch
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Yanzu-Yanzu: An yi wa shugaban kasar Haiti kisar gilla a gidansa

A cewar Omejalile, wanda ake zargin da aka fi sani da Bola Bebo, wanda ke ikirarin shi shugaban tashar mota na Iyana Iba ne ya dade yana cika bakin cewa babu wanda ya isa ya kama shi.

SaharaReporters ta ruwaito cewa Omejalile ya ce baya da matarsa da yarsa, ya kuma shafawa wasu mata 12 cutar da HIV ga gangan.

Ya ce:

"Da gangan ya ke yi kuma baya nadama, an sha kama shi amma sai ya bada cin hanci ya fito ya koma ya rika musgunawa wadanda ya shafawa cutar.
"Na baya-bayan nan shine matarsa Mrs Bolaniran, wacce ya ke musgunawa bayan ya shafamata cutar. Ya kuma shafa wa yarta cutar.
"Da farko an nemi yan sandan Igando su kama shi amma hakan bai yiwu ba.
"Amma daga bisani an kama shi an kashi sashin binciken manyan laifuka na SCIIDda ke Panti."

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kashe mutum 19 a Katsina, sun ƙona gidaje sun sace dabbobi masu yawa

Kungiyar direbobi ta nesanta kanta da Bolaniran

Kungiyar direbobi na kasa NURTW ta nesanta kanta da Bolaniran tana mai cewa ba mambanta bane kuma bai taba yin rajista da ita ba.

Sakataren kungiyar na Legas, Oluwaseyi Bankole ya bayyana hakan yayin da ya ke martani game da labarin Bolaniran da ya bazu a gari cewa yan sandan sun kama shi saboda yana shafawa mata cutar kanjamau.

'Yan Bindiga Sun Sace Mata 13 a Hanyarsu Ta Zuwa Biki a Birnin Gwari

A wani labarin, yan bindiga sun sace mata 13 a tsakanin garuruwan Manini da Udawa da ke kan babban hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna, a hanyarsu ta zuwa bikin daurin aure, Daily Trust ta ruwaito.

Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis misalin karfe 12 na rana a lokacin da yan bindigan suka tare motocci uku da ke dauke da matan a hanyarsu ta zuwa Birnin Gwari.

An gano cewa cikin wadanda aka sace din akwai mata masu shayarwa da wata mata da yayanta mata biyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164