Da duminsa: Allah ya yiwa Wazirin masarautar Hadejia rasuwa

Da duminsa: Allah ya yiwa Wazirin masarautar Hadejia rasuwa

  • Wazirin Masarautar Hadejia dake jihar Jigawa ya rigamu gidan gaskiya
  • Dattijon ya rasu ne bayan gajeriyar rashin lafiya da daren Laraba
  • An shirya jana'izarsa a kofar fada bayan Sallan Azahar

Allah yayi wa Maigirma Wazirin Hadejia, Alh. Hashim Amar rasuwa.

Rahoton da Legit ta samu daga shafin Masarautun Arewa yace za'ayi Janaiza karfe 1.30 na rana a kofar Masallachin Mai martaba Sarkin Hadejia.

Daya daga cikin 'yan uwan mamacin, Jamilu Isyaku, ya bayyana cewa Wazirin ya rasu ne da daren Laraba bayan gajeruwar rashin lafiya.

Jamilu ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook.

Yace:

"Ina mai sana da mutuwar baffana Alha Hashim Amar (wanda akafi sani da Wazirin Hadejia) bayan gajeriyar rashin lafiya da daren jiya."

Kara karanta wannan

Shekaru 8 da kashe Sheikh Albani Zaria, an cika masa burinsa na kafa gidan talabijin

"Allah ya azurtashi da Jannatun Frdausi."
Da duminsa: Allah ya yiwa Wazirin masarautar Hadejia rasuwa
Da duminsa: Allah ya yiwa Wazirin masarautar Hadejia rasuwa
Asali: Facebook

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng