Mutum 9 sun mutu, 41 sun jikkata sakamakon hatsarin mota a Kano

Mutum 9 sun mutu, 41 sun jikkata sakamakon hatsarin mota a Kano

- Hatsarin mota ya yi sanadin rasuwar mutanen 9 a Kunar Damawa a Kano

- Shugaban FRSC na Kano ya ce ɓacin birki ne ya yi sanadin mummunar hatsari

- Cikin waɗanda suka rasu akwai maza uku, mata shida sai mutum 41 da suka jikkata

Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa, FRSC, ta tabbatar da rasuwar mutum 9 sakamakon hatsarin mota da ta faru a Kunar Damawa a ƙaramar hukumar Ɗanbatta a Kano, rahoton PM News.

Da ya ke tabbatar da hatsarin a ranar Lahadi, kwamandan hukumar a Kano, Zubairu Mato, ya ce mutum 41 sun kuma jikkata a hatsarin.

DUBA WANNAN: Za ka ɗaukaka a siyasa: Martanin tsohon gwamnan PDP kan tuɓe Ɗawisu da Ganduje ya yi

Mutum 9 sun mutu, 41 sun jikkata sakamakon hatsarin mota a Kano
Mutum 9 sun mutu, 41 sun jikkata sakamakon hatsarin mota a Kano. Hoto: @daily_trust
Asali: UGC

"An kira mu misalin ƙarfe 4.10 na yamma, ranar Lahadi, don haka muka aika jami'an mu cikin gaggawa zuwa inda abin ya faru don ceto wadanda hatsarin ya rutsa da su tare da kawar da abubuwan da ke titin," in ji Mato.

Ya ce hatsarin ya faru ne saboda lalacewar birkin ɗaya daga cikin direbobin.

KU KARANTA: Tsaro: 'Yan bindiga sun kashe mutane bakwai a jihar Kaduna

A cewarsa motoci uku hatsarin ya ritsa da su - babban mota mai lamba XA 111 SNN, Volkswagen Golf 3 mai lamba DAL 515 ZX da Mercedes Benz mara lamba.

"Wadanda suka rasu sun hada da maza uku, mata Shida sai kuma mutum 41 da suka jikkata," in ji shi.

Shugaban na FRSC ya ce an kai wadanda abin ya ritsa da su babban Asibitin Ɗanbatta inda likitan da ke aiki ya tabbatar mutum 9 sun mutu.

A wani labarin daban, ofishin mai bawa Shugaban Kasa shawara kan Tsaro da Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Isa Ali Pantami, a jiya sun sha banban kan kaddamar da fasahar sadarwa ta 5G a Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

Sun yi magana ne a Abuja yayin wani taro da kwamitocin Majalisar Dattawa kan Sadarwa, Kimiyya da Fasaha, da Yaki da Laifukan Yanar Gizo da Lafiya da Cututtuka masu Yaduwa suka shirya kan matsayin fasahar 5G.

A yayin da Pantami ya ce Najeriya ta shirya tsaf domin kaddamar da fasahar 5G, ofishin NSA ta nuna damuwarta kan wasu matsaloli da ke tattare da fasahar.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel