Wata sabuwa: 'Yan bindiga ta'addanci kadai suke aikatawa, ba 'yan ta'adda bane, inji Gumi
- Fitaccen malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana yadda ake cutar da Fulani makiyaya
- Ya kuma bayyana cewa, 'yan bindiga da ke aikata ta'addanci ba 'yan ta'adda bane, domin ba su da laifi
- Ya kuma bayyana irin rashin adalci da ake yiwa Fulani makiyaya har ya kai ga suka fara daukar makami
Najeriya - Shahararren malamin addinin musuluncin nan, Sheikh Ahmad Gumi, ya ce ‘yan bindiga suna aikata ta’addanci amma su ba ‘yan ta’adda ba ne.
Gumi ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da jaridar Daily Trust.
Ya ce kiraye-kirayen da ake yi na gwamnati ta ayyana ’yan bindiga a matsayin ’yan ta’adda ba komai bane face rashin adalci da son zuciya.
Ya yi magana ne gabanin wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya shaida wa makilin Daily Trust cewa:
“Wannan abin takaici ne ta hanyar rashin adalci da son zuciya. IPOB kungiya ce, ba tana nufin Igbo ba. Boko Haram kungiya ce kuma ba tana nufin Kanuri ba.
“Don haka za ku iya ayyana ‘yan Boko Haram a matsayin 'yan ta'adda, kuna iya ayyana ‘yan IPOB a matsayin 'yan ta'adda. A wannan yanayin me za ku ayyana 'yan ta'adda?
“'Yan bindiga kwatance ne mara tushe. Me kuke bayyanawa? Kuna so ku ce makiyaya ’yan ta’adda ne? Wannan daya kenan. Na biyu kuma, yanzu an ayyana IPOB a matsayin 'yan ta’adda, ta yaya aka samu canji? Amurka, Tarayyar Turai, a ko'ina ba su amince da wannan furucin ba.
“Ba su sanya musu takunkumi ba, hana su tafiye-tafiye ba, ba da gudummawar kudi ba, watakila saboda ba mu ba ne, su ne.
“Kuma a wannan yanayin, idan kuka ce Fulani makiyaya ‘yan ta’adda ne domin wannan ita ce maganar da kuka fada, ba za ku iya cewa ‘yan bindiga ‘yan ta’adda ba ne, ‘yan bindiga suna aikata ta’addanci amma su ba ‘yan ta’adda ba ne."
Kisan gillar da ake yi wa Fulani shi ke rura wutar fitina
A cewar Gumi, kashe-kashen da ake yi wa Fulani ba bisa ka’ida ba shi ne babban abin da ke kara rura wutar rikicin ‘yan bindiga a kasar nan.
Ya kara da cewa:
“Za a iya kama Bafulatani da bai ji ba bai gani ba bisa zarginsa kuma ya rasa shanunsa, kamar yadda ‘yan bindiga za su yi garkuwa da wanda bai ji bai gani ba, ya rasa dukiyarsa.
"Don haka duk mutanen da ke rike da bindigogi a yanzu suna da alhakin cin zarafi da cutar da mutane, ko dai a bangaren gwamnati ko kuma..."
“Kai, bari ma suna ba da hujjar abin da suke yi daga abin da ya faru da mutanensu a hannun jami’an tsaro macuta.
“Ban ce duk jami’an tsaro haka suke ba amma daga macuta da muke da su kuma da wannan abin da ya farun suka ce ‘shikenan zamu rama’ shi ya sa ba su da wani nadama kan aikata ko daya daga cikin wadannan laifuka.
"Ba ku san laifukan da aka aikata a kansu ba, hatta kisan kiyashi an yiwa Fulani makiyaya."
Sheikh Gumi ya bayyana yadda 'yan bindiga suka fi gwamnati son ganin karshen ta'addanci
A wani labarin, Sheikh Ahmed Gumi, shahararren malamin addinin Islama a Najeriya ya bayyana cewa, 'yan bindiga sun fi kaunar a kawo karshen ta'addanci fiye da gwamnati.
Malamin ya bayyana haka ne yayin wata hira da jaridar Daily Trust, inda ya bayyana kokarinsa na shawo kan 'yan bindiga domin su bar aikata barna su zauna da kowa lafiya.
Gumi ya daura laifukan da suke faruwa na rashin tsaro ga gwamtocin kasar nan, inda ya bayyana cewa, a cikinsu akwai wadanda suke amfana da tashe-tashen hankula shiyasa basa son batun ya mutu.
Asali: Legit.ng