Kano: 'Yan Hisbah sun ƙwace Whot daga hannun matasa, sun basu Kur'ani su karanta

Kano: 'Yan Hisbah sun ƙwace Whot daga hannun matasa, sun basu Kur'ani su karanta

  • Rundunar Hisbah reshen jihar Kano ta kama wasu taron matasa su na yin wani fitaccen wasa na kati wanda ake kira da Whot
  • Sun kama matasan bisa zarginsu da laifin bata lokacinsu su na wasan maimakon yin abubuwa masu muhimmanci da zasu amfanesu
  • Lamarin ya auku ne a garin Warawa, inda suka wuce da matasan ofishinsu sannan su ka raba musu fallayen Qur’ani don su karanta

Jihar Kano - Rundunar Hisbah reshen jihar Kano ta yi ram da wasu matasa da jami’anta su ka kama su na yin wasan kati na Whot, jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

An kama matasan ne suna bata lokutan su wurin yin wasanni maimakon yin abubuwan da za su amfane su.

Read also

Zamfara: 'Yan bindiga sun tayar da wani ƙauye bayan sun yi wa mutum 7 kisar gilla

Kano: 'Yan Hisbah sun ƙwace Whot daga hannun matasa, sun basu Kur'ani su karanta
Matasan da Hisbah ta kwace Whot a hannunsu ta basu Kur'ani su karanta. Hoto: Daily Nigerian
Source: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daily Nigerian ta ruwaito yadda hukumar ta raba wa matasan wasu fallaye daga Qur’ani kuma ta umarcesu da su karanta.

Kwamanda janar na Hisbah, Dr Muhammad Haroon Ibn Sina ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook cewa:

“Ofishin Hisbah na Warawa sun kama wasu matasa bisa zarginsu da bata lokutansu wurin yin wasan kati na Whot.
“Don haka ne hukumar ta raba musu wasu fallaye daga Qur’ani mai girma don su yi amfani da lokutansu su karanta.”

Dama hukumar ta dade tana kafa dokoki iri-iri

A watan Augustan da ya gabata ne rundunar ta haramta amfani da mutummutumi a jihar, a cewarsu hakan ci gaba da samar da gumaka ne.

Ibn Sina ya shaida cewa:

“Musulunci ya yi hani da sassaka gumaka. Yanayin kan mutum-mutumin yana kama da mutane.”

Read also

Fuskokin wasu kasurguman masu garkuwa da mutane da aka yi ram dasu a jihar Ribas

A watannin baya da suka gabata ne Hisbah ta kama wani matashi akan yin wani aski wanda ta ce bai dace da tsarin jihar ba.

Kano: Motar Giya Ta Faɗi Kusa Da Ofishin Hisbah, Wasu Sun Ƙi Kai Dauƙi Don Gudun Fushin Allah

A wani rahoton, wata mota kirar Hilux da ke dauke da barasa ta fada cikin kwata da ke daf da ofishin Hisbah a Panshekara, karamar hukumar Kumbotso na jihar Kano.

An rahoto cewa lamarin ya faru ne a yammacin ranar Talata 16 ga watan Nuwamba kuma direban motar ya jikkata.

Mazauna yankin sun garzaya domin kai wa mutanen da ke cikin motar dauki ne sannan suka gano ashe giya ne makare cikin motar.

Source: Legit.ng

Online view pixel