A cigaba da garkame Abdul-Jabbar, Kotun Shari'a ta sake hana beli Shehin Malami

A cigaba da garkame Abdul-Jabbar, Kotun Shari'a ta sake hana beli Shehin Malami

  • Tun watan Yuli, hukuma ta tsare shehim Malami, Sheikh AbdulJabbar Nasiru Kabara a jihar Kano
  • Gwamnatin jihar Kano ta shigar da AbdulJabbar kotun Shari'a ne kan zargin kalaman batancin da basu dace ba
  • Wannan ya biyo bayan mukabala da Gwamnatin jihar ta shirya tsakanin Malamin da sauran Malaman jihar Kano

Kano - Kotun Shari'ar Musulunci dake zamanta a Kofar Kudu a jihar Kano ta sake hana Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara beli bayan watanni da tsareshi, rahoton BBC Hausa.

Muhammad A Mika’il, wanda ke wakiltan Malam AbdulJabbar a kotu ya sake gabatar da bukatar gaban mai Shar'ia Ibrahim Sarki Yola a zaman kotun da aka yi ranar Alhamis, 25 ga Nuwamba, 2021.

BBC ta rahoto cewa Gwamnatin jihar Kano ta bi umurnin da kotu tayi na cewa a baiwa Malam AbdulJabbar kudi N20,000 don ya sayi litattafai kuma a kawo masa littafin Sahihul Bukhari da Sahihu Muslim.

Kara karanta wannan

Shugaban karamar hukuma a Kano ya fada hannun ICPC, ana zargin ya ci makudan kudi

Kotu tace za'a yi zama na gaba ranar 9 ga watan Disamba, 2021.

Kotun Shari'a ta sake hana beli Shehin Malami
A cigaba da garkame Abdul-Jabbar, Kotun Shari'a ta sake hana beli Shehin Malami Hoto: BBC Hausa
Asali: UGC

Na janye kalamaina: Abduljabbar ya amince malaman Kano sun yi nasara a kansa

Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya bayyana cewa, a yi masa afuwa kuma lallai ya janey maganganun da ya yi game Manzon Allah SAW wadanda ake ganin sun taba mutuncin ma'aiki.

A cikin wani sauti karo na biyu da ya aike wa sashen Hausa na BBC ranar Lahadi, malamin ya ce yana fatan "hakan ya zama silar gafara da rahama da jin kai gare ni".

Ya kara da cewa:

"Wadannan maganganu da suka fito daga bakina suka jawo ce-ce-ku-ce game da Ma'aiki SAW, na janye su na kuma janye su."

Wannan ya faru ne 'yan awanni bayan sautin farko da ya fitar a Lahadin yana neman afuwar wadanda suka fahimci cewa shi ne ya kirkiri kalaman batanci ga Annabi da ake zarginsa da yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel