Sokoto: Sojoji sun yi lugude a kan 'yan bindiga, sun samo makamai da babura

Sokoto: Sojoji sun yi lugude a kan 'yan bindiga, sun samo makamai da babura

  • Sojoji sun halaka ‘yan bindiga da dama bayan musayar wutar da ta shiga tsakaninsu a kauyen Kuzari da ke karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto a ranar Talata
  • ‘Yan bindigan sun harbi wani soja a kafa wanda aka yi gaggawar wucewa da shi asibitin sojoji da ke cikin Sokoto don duba lafiyarsa
  • Wata majiya ta bayyana yadda sojojin suka samu nasarar kwatar makamai da babura daga ‘yan bindigan wadanda daga baya aka babbaka a kauyen

Sokoto - Sojoji sun samu nasarar halaka ‘yan bindiga da dama sakamakon wata musayar wuta da su ka yi a kauyen Kuzari da ke karamar hukumar Sabon Birni a cikin jihar ranar Talata.

An samu rahoto akan yadda suka harbi wani soja a kafa wanda aka wuce dashi asibitin soji da ke Sokoto don kulawa da lafiyarsa.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Masu garkuwa sun kashe tsohon mai neman takarar gwamnan Zamfara a hanyar Abuja zuwa Kaduna

Sokoto: Sojoji sun yi lugude a kan 'yan bindiga, sun samo makamai da babura
Sokoto: Sojoji sun yi lugude a kan 'yan bindiga, sun samo makamai da babura. Hoto daga BBC.com
Asali: UGC

Wata majiya ta sanar da Daily Trust cewa sojojin sun samu nasarar kwatar makamai da babura daga hannun ‘yan bindigan.

Daga baya aka banka wa baburan wuta a cikin kauyen.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daya daga cikin ma’aikatan da aka yi batakashi da shi, ya ce ‘yan bindigan sun bude wuta iyakar yadda zasu iya.

“Muna tsaka da sintiri a wuraren Sabon Birni da ‘yan bindiga suka addaba kawai muka gan mu a tsakiyarsu a kauyen Kuzari da ke gundumar Kurawa.
“Nan sojoji suka fara musayar wuta da su wanda aka yi kusan sa’a daya ana yi kafin su zubar da makamansu su tsere.
“A nan sojojin suka halaka ‘yan bindiga da dama sannan suka samu makamai da babura da dama. Daga baya aka tattara baburan sannan aka banka musu wuta,” a cewarsa.

Yace an samu babura 10, sannan sun kuma harbi wani soja a kafarsa wanda yake asibitin soji da ke Sokoto yanzu haka ana duba lafiyarsa.

Kara karanta wannan

Katsina: ‘Yan bindiga sun halaka jaruman ‘yan sanda 2 yayin musayar wuta

Sai dai ba a sanar da yawan ‘yan bindigan da aka halaka ba, inda yace mazauna yankin ne kadai zasu iya fadin yawan gawawwakin da aka fitar daga dajin.

Sabon Birni ta na fuskantar farmaki iri-iri tun tsawon shekaru inda ake ta halaka mazauna da dama, a yiwa wasu fyade sannan a yi garkuwa da wasu.

Fiye da mutane 50,000 sun bar gidajensu saboda ‘yan bindiga kuma yanzu haka sun nemi wurin zama a garuruwan da ke makwabtaka da jamhuriyar Nijar.

Wata majiya mai karfi ta tabbatar wa da Daily Trust cewa, sojojin sama sun halaka iyaye da matar Bokkolo, wani hatsabibin dan bindiga a wuraren Isa zuwa yankin Sabon Birni a makon da ya gabata.

An tattaro bayanai akan yadda hatsabibin ya samu kubucewa daga harin amma an samu nasarar halaka yaransa da dama a ranar Asabar.

Ku halaka 'yan bindiga, ku kawo gawawwakinsu da makamansu, COAS ga dakarun soji

Kara karanta wannan

Sabon farmakin da 'yan fashin daji suka kai Sokoto ya lamushe rayuka 14

A wani labari na daban, shugaban sojin kasa na Najeriya, Laftanal Janar Farouk Yahaya, ya umarci dakarun sojin Najeriya da su bindige 'yan bindiga da 'yan ta'adda tare da kawo gawawwakinsu da makamansu.

Daily Trust ta ruwaito cewa, ya bayar da wannan umarnin ne a yayin ziyarar da ya kai wa birged ta 31 ta horarwa, TRADOC da ke Minna inda ya kaddamar da rukunin dakunan kwanan hafsoshin sojoji matafiya a ranar Lahadi.

"Na zo Niger a yau ne a cikin wani ziyarar aiki na 31 Artillery Brigade da TRADOC. Na jinjinawa dakarun kan ayyukan da suke yi. Kada ku sassauta, ku cigaba kuma kada ku sassauta wa 'yan ta'adda."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng