Kada ka janye dokar hana shigo da shinkafar kasar waje, Gwamnan APC ga Buhari

Kada ka janye dokar hana shigo da shinkafar kasar waje, Gwamnan APC ga Buhari

Jihar Ondo - Gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu, ya bukaci Shugaba Muhammadu Buhari kada ya janye dokar hana shigo da shinkafar kasashen waje da ya saka.

Akeredolu ya ce Nigeria tana da karfin da za a iya samar da shinkafa domin samar da ayyuka har ma a rika fita da shi kasashen duniya, The Nation ta ruwaito.

Ya yi wannan jawabin ne yayin da ya ke duba shinkafar da aka girbe a Akure da kewaye tare da hadin gwiwar Cibiyar Noma na Zamani, NCAM, da ke amfani da wani fasaha na kasar Japan mai suna 'Sawah Eco-technology' don noma shinkafa.

Kada ka janye dokar hana shigo da shinkafar kasar waje, Gwamnan APC ga Buhari
Kada ka janye dokar hana shigo da shinkafar kasar waje, Akeredolu ya fadawa Buhari. Hoto: The Nation
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

Gwamnati ta fara rabawa talakawa kudi N1.6bn a jihar Jigawa

Babban lauyan na Nigeria, SAN, ya bayyana gamsuwarsa kan cewa jiharsa za ta iya rike kanta a bangaren noman shinkafa idan aka cigaba da amfani da fasahar.

Gwamnan da ya samu wakilcin mashawarcinsa na musamman a bangaren noma da kasuwancin noma, Mr Akin Olotu, Akeredolu ya ce gwamnatin jihar ba za ta tsinduma cikin noman shinkafa ba amma za ta yi aiki tare da monoman wurin amfani da fasahar Sawah don bunkasa noman shinkafa.

Jaridar ta rahoto cewa ya yi bayanin cewa fasahar za ta bawa manoma daman shuka shinkafa su kuma girbe har sau uku a cikin shekara guda don haka manoman za su samu karin riba.

"Muna da fadama sosai a jihar mu. Fadamar ya fi hekta 20,000 kuma wannan fasahar ya nuna abinda za a iya samu a hekta 1. Manomi zai iya samun Naira miliyan 1.8 a hekta 1 da wannan fasahar.
"Buhari ya yi jarumta da ya hana shigo da shinkafa. Bai kamata muna shigo da shinkafa ba. Muna samarwa wasu kasashen aikin yi amma yanzu akwai aikin a nan kuma ya kamata matasan mu su shiga a yi da su a maimakon neman aikin ofis," a cewar sa.

Kara karanta wannan

Innalillahi: An tsinta gawar limamin Abuja kusa da gona

Martanin Shugaban Sawah na Nigeria

Shugaban Fasahar Sawah Technology na Nigeria, Dr Ademiluyi Yinka ya ce Shugaba Buhari ya bada umurnin a horas da manoma a wasu zababun jihohi a karkashin NCAM.

Dr Ademiluyi ya ce fasahar tana samar da shinkafa fiye da yadda manoma ke samu a baya kuma tana bada daman magance ciyawa da kwari cikin sauki.

Ana bin kowanne ɗan Najeriya bashin N64,684 bisa basukan da ƙasar ta ci a ƙasashen waje

A wani labarin, kun ji cewa bisa yawan ‘yan Najeriya da kuma yawan basukan da ake bin ta, kowa ya na da N64,684 a kan sa.

Kamar yadda kowa ya san yawan bashin da Najeriya take ta amsowa daga kasashen ketare, yanzu ko wanne dan Najeriya ya na da bashin $157 ko kuma N64,684 a kan sa.

Bisa wannan kiyasin, masanin tattalin arzikin kasa, Dr. Tayo Bello ya bayyana damuwar sa akai inda ya ce duk da zuzurutun basukan, babu wasu abubuwan ci gaba da aka samar wadanda za su taimaka wurin biyan basukan kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164