Da duminsa: Gwamnonin APC sun shiga ganawar sirri a Abuja

Da duminsa: Gwamnonin APC sun shiga ganawar sirri a Abuja

Gwamnanonin jihohin Najeriya dake jam'iyyar All Progressives Congress (APC) sun shiga ganawar sirri a gidan ajiya bakin Gwamnan jihar Kebbi dake Abuja, ranar Lahadi, 21 ga Nuwamba 2021.

Daily Trust ta ruwaito cewa majiyoyi sun ce zaman bai rasa nasaba da lamarin taron gangamin jam'iyyar da ake shirin yi.

Wadanda ke hallare a tarin sun hada da Shugaban kungiyar gwamnonin kuma gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu; Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule; da Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq.

Hakazalika akwai Gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari; Gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong; Gwamnan jihar Jigawa, Abubakar Badaru da Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje.

Sauran sune Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimna; Gwamnan Borno, Babagana Zulum; Gwamnan Ebonyi, Dave Umahi; Gwamnan Legas, Babajide Sanwoolu; Gwamnan Neja, Abubakar Sani Bello; Gwamnan Ogun, Dapo Abiodun; Gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi; da Gwamnan Cross River, Ben Ayade.

Kara karanta wannan

Ka cancanta: Jami'ar Afe Babalola ta karrama Zulum da digirin digirgir

Da duminsa: Gwamnonin APC sun shiga ganawar sirri a Abuja
Da duminsa: Gwamnonin APC sun shiga ganawar sirri a Abuja
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Asali: Legit.ng

Online view pixel