An shiga halin fargaba a jihar Neja yayin da ‘yan bindiga suka sace wani dan kasuwa dan kabilar Igbo

An shiga halin fargaba a jihar Neja yayin da ‘yan bindiga suka sace wani dan kasuwa dan kabilar Igbo

  • 'Yan bindiga sun kai hari garin Maikunkele a karamar hukumar Bosso da ke jihar Neja inda suka yi awon gaba da wani dan kasuwa dan kabilar Igbo
  • Maharan sun kai hari garin tare da yin harbi a sama domin tsorata mutane kafin suka sace wanda suke hari
  • Tuni hakan ya haddasa fargaba a tsakanin mazauna garin Minna, saboda kusancin garin da babbar birnin jihar

Jihar Neja - Wasu tsagerun 'yan bindiga sun kai farmaki garin Maikunkele, da ke wajen birnin Minna a karamar hukumar Bosso da ke jihar Neja sannan suka yi awon gaba da wani dan kasuwa dan kabilar Igbo.

An tattaro cewa maharan su da yawa sun kai farmaki yankin daga wani daji da ke kusa da filin jirgin saman Minna, inda suka ta harbi a iska don tsoratar da jama'a kafin suka dauke mutumin.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: 'Yan bindiga sun yi wa mutane 7 kisar gilla a Tor-Togan

An shiga halin fargaba a jihar Neja yayin da ‘yan bindiga suka sace wani dan kasuwa dan kabilar Igbo
An shiga halin fargaba a jihar Neja yayin da ‘yan bindiga suka sace wani dan kasuwa dan kabilar Igbo Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Jaridar Tribune ta rahoto cewa sace dan kasuwar na zuwa ne kasa da shekara guda bayan wani dan Igbo ya rasa ransa a wani lamari makamancin wannan.

Yayin da suke ta harbi ba tare da an kalubalance su ba, mazauna yankin sun tsere domin tsiratar da ransu. Da dama sun gudu zuwa dazazzukan da ke kusa yayin da wasu suka fake a wata kasuwar mako da ke kusa.

Tuni wannan ya haifar da fargaba a garin Minna, babbar birnin jihar da kewaye yayin da labarin sace dan kabilar Igbon wanda ya kasance dan jihar Enugu ya bazu, rahoton jaridar Independent.

Ana tsoron kada maharan sun shiga babbar birnin jihar duk da tabbacin da hukumomin tsaro da gwamnatin jihar suka basu na kare rayuka da kayayyaki.

Kara karanta wannan

Kano: Motar Giya Ta Faɗi Kusa Da Ofishin Hisbah, Wasu Sun Ƙi Kai Dauƙi Don Gudun Fushin Allah

Ba a samu jin ta bakin jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan jihar Neja, DSP Wasiu A. Abiodun ba don tabbatar da harin.

Sai dai kuma, shugaban kungiyar Ohanaeze Ndigbo, reshen jihar Neja, Cif Emmanuel Ezeugo, ya tabbatar da sace dan Igbon wanda ba a tabbatar da sunansa ba a daidai lokacin kawo wannan rahoto.

"Zan iya tabbatar maku da cewa yan bindiga sun sace wani dan Igbo da ke siyar da kayayyaki a Maikunkele. Irin haka ya faru a shekarar da ta gabata lokacin da aka sace wani dan Igbo a wani lamari makamancin haka."

Gwamnati ta haramta siyar da babura a wata jihar arewa

A wani labarin, mun kawo a baya cewa gwamnatin jihar Neja ta haramta siyar da babura a cikin jihar.

Babban sakataren gwamnatin jihar, Ahmed Ibrahim Matane, wanda ya sanar da hakan a cikin wani jawabi a ranar Asabar, ya ce hukuncin ya biyo bayan matsalolin rashin tsaro da ake fama da su a wasu yankunan jihar.

Kara karanta wannan

An tafi har gida an bindige Shugaban kamfanin Three Brothers Mill da matarsa a Jigawa

Ya kuma ce an dauki matakin ne saboda bukatar da ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane ke gabatarwa na neman a basu babura a matsayin fansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng