Limamin Abuja: Yadda masu shekaru 17 zuwa 19 suka sace ni tare da azabtar da ni
- Limamin masallacin Yangoji da ke Kwali a Abuja, Abdullahi Abubakar Gbedako, ya bayar da labarin yadda wadanda suka sace shi suka azabtar da shi
- Malamin makarantar ya sanar da yadda iyalinsa suka siyar da motarsa tare da ta kaninsa da ke kauye kuma suka ari bashi N1.5m domin fansarsa
- Abun takaicin kamar yadda ya sanar, yara matasa ne masu shekaru daga 17 zuwa 19 ne dauke da bindiga suka sace shi tare da gana mishi azaba
FCT, Abuja - Babban limamin masallacin Ƴangoji da ke ƙaramar hukumar Kwali ta Abuja, ya bayyana uƙuba tare da azabar da ya sha a hannun wadanda suka sace shi.
Daily Trust ta ruwaito cewa, Liman Abdullahi Abubakar Gbedako, wanda aka sace tare da ɗan shi, ya kwashe makonni uku a hannun masu garkuwa da mutane kuma an sako shi bayan an biya kuɗin fansa har N5 miliyan.
A yayin bayani game da azabar da ya sha a hannun miyagun a gaban manema labarai, limamin wanda shi ne mataimakin shugaban makarantar GJSS Kwaita, ya ce shi da ƴaƴanshi sun matuƙar shan wahala, Daily Trust ta wallafa.
Ya ce shi da ƴaƴan shi maza biyu sun kwashe kwanaki huɗu a daji kafin wadanda suka sace su su umarcesu da su cigaba da tafiya har sai da suka kai sansaninsu inda suka kwashe kwanaki tara.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Gbedako yace, "Tun kafin mu tsallake wani babban rafi ne maciji ya sari ɗa na kuma hakan yasa na dauke shi a bayana domin tsallake rafin kafin ya samu ya tsere bayan mun isa sansanin."
Kamar yadda yace, masu garkuwa da mutanen sun ɗaure musu hannaye da kafafu kuma suna rufe musu fuska da ƙyalle da rana amma sai su buɗe musu da dare.
Karin Bayani: Bayan harin Islamiyya, Tsagerun yan bindiga sun sake mamaye Tegina, sun sace ma'aikata
Ya ce ya umarci iyalansa da su siyar da motarsa da ta ƙaninsa da ke ƙauye kuma su samo bashin miliyan daya da rabi domin biyan kuɗin fansan.
"A yanzu da nake muku magana, ba ni da kadara ko ɗaya. Amma ina godiya ga Allah da ya bar ni da rai na sa ta ɗa na," yace.
"Babban abun takaicin shi ne, masu garkuwa da mutanen duk yara ne masu shekaru daga 17 zuwa 19. Kuma babban makaminsu shi ne waya da bindigar da suke dauke da ita, wacce na yarda cewa jami'an tsaronmu za su iya nemo inda suke tare da dasa musu bama-bamai."
Ya ce bayan ƴan bindigan sun shiga gidansa kuma suna jagorantarsa da ƴaƴansa biyu zuwa dajin, ɗaya daga cikin masu garkuwa da mutanen ya tambaye shi Qur'anai nawa gare shi a gida, sai yace kowa a gidansa ya na da Qur'ani.
"Bayan nan wani ya sake tambaya ta wane ne limamin, sai nace musu ni ne. Sai cewa yayi tunda ni ne babban limamin, in bayar da miliyan goma domin su sake ni, amma na sanar mishi ba ni da ko miliyan ɗaya," yace.
Sai dai, babban limamin ya yi kira ga gwamnati da ta kawo masa ɗauki domin ya fara sabuwar rayuwa.
Asali: Legit.ng