Barawon waya ya mutu cikin Kurkuku yayin rikicin zama shugaban Fursunoni

Barawon waya ya mutu cikin Kurkuku yayin rikicin zama shugaban Fursunoni

  • Wani barawon waya da aka jefa Kurkuku ya shiga rikici da wadanda ya tarar cikin kan wanda zai zama Shugaba
  • Da alamun bai samu nasara a wannan rikici ba kuma ya rasa rayuwarsa sakamakon wannan rikici
  • Jami'in dan sandan da ke lura da shi ya garzaya da shi asibiti inda yayi numfashinsa na karshe

Abuja - Kwamitin bincike kan zaluncin yan sandan EndSARS a ranar Laraba ta saurari bayanin yadda wani barawon waya, Ogaga Ohore, ya rasa rayuwarsa a sakamakon rikici cikin Kurkuku.

Dan sandan da yayi jawabi, Edwin Ekeinde, ya bayyana cewa an jefa Ohore cikin Kurkuku kan laifin kwace waya kirar Techo hannun Sunday Adache, rahoton Punch.

A cewarsa, Ohore ya mutu daga baya a asibitin jami'ar Abuja dake Gwagwalada hannun yan sanda sakamakon rikicin da ya barke tsakaninsa da wasu fursunoni saboda yana son zama shugabansu.

Kara karanta wannan

Masu garkuwa da mutane sun kashe wani kyaftin din soji mai ritaya

Yace:

"A ranar 13 ga Junairu, 2020, an bibiya wayar sata zuwa hannun wani Destiny Temitope, wanda aka damkeshi kuma ya kai jami'anmu wajen wanda ya sayar masa da waya mai suna Joshua Auta."
"A ranar, Joshua Auta bayan shan tambayoyi ya kai yan sanda wajen Ogaga Ohore. kuma muka damkeshi"

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Barawon waya ya mutu cikin Kurkuku yayin rikicin zama shugaban Fursunoni
Barawon waya ya mutu cikin Kurkuku yayin rikicin zama shugaban Fursunoni
Asali: UGC

Lokacin da ya fara rashin lafiya

Jami'in dan sandan ya cigaba da cewa:

"A ranar 23 ga Maris, 202, na samu kiran waya daga ofishin yan sanda cewa Ohore bai da lafiya. Sai na kaishi asibiti a Area 1, Garki inda yayi jinya sannan na mayar da shi kurkukun."
"Ohore da kansa ya fada min akwai rikici tsakaninsa da Fursunonin da suka girmesa. Ohore na son zama Shugaban fursunoni. Hakan ya haddasa rikici cikinsu."
"Bayan kwana biyu na sake samun labarin ya sake rashin lafiya."

Kara karanta wannan

Kisan babban jami'an soja a Kaduna: Makwabcinsa ya bayyana gaskiyar wadanda suka kashe shi

"Sai aka kaishi asibitin koyarwan Jami'ar Abuja, Gwagwalada, inda ya mutu bayan wasu sa'o'i."

Asali: Legit.ng

Online view pixel