Mun samu rahoton satar amsar jarabawa 15,000 a jihar Bauchi, Kwamishina

Mun samu rahoton satar amsar jarabawa 15,000 a jihar Bauchi, Kwamishina

  • Kwamishinan ilimi na jihar Bauchi, Aliyu Tilde, ya bayyana cewa satar amsar jarabawa ta zama ruwan dare a jihar
  • A cewarsa daga ranar 8 ga watan Nuwamba da aka fara jarabawar BECE 2021, an samu rahoton satar amsa 15,000 a faɗin jihar
  • Yace ya zama wajibi a shirya wa ɗaliban wata jarabawa bayan wannan kuma za'a ɗau mataki kan manyan jami'ai

Bauchi - Punch ta rahoto cewa aƙalla sau 15,000 aka samu rahoton satar amsar jarabawa a jihar Bauchi yayin gudanar da jarabawan shiga babbar sakandire BECE ta shekarar 2021.

Kwamishinan Ilimi na jihar Bauchi, Aliyu Tilde, shine ya bayyana haka ga manema labarai a wani taro da ya kira ranar Laraba.

Yace ɗalibai 52,000 suka zauna jarabawar BECE 2021, yayin da 45,000 daga cikinsu sun fito daga makarantun gwamnati.

Kara karanta wannan

Mambobin jam'iyyar PDP Mata sama da 3,000 sun koma jam'iyyar APC a jihar Arewa

Jihar Bauchi
Mun samu rahoton satar amsar jarabawa 15,000 a jihar Bauchi, Kwamishina Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Kwamishinan ya bayyana cewa a cikin wannan adadin, an samu matsalar satar jarabawa sau 15,000 a bangaren Essay.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Guardian ta rahoto Tilde yace:

"Ina da shaidar hoton bidiyo na satar jarabawan da aka yi a yakina, ba wai zamu hukunta daliban bane, amma zamu hukunta waɗan da muka wakilta su kula da su."
"Kuma ba zamu sake barin su, su gudanar da wata jarabawa ba a gaba, wannan ne kaɗai matakin da zamu iya ɗauka, kuma zamu ɗauka."

Wane mataki za'a ɗauka kan ɗaliban?

Kwamishinan ya ƙara da cewa ya zama wajibi su shirya wa ɗaliban gwaji, inda yace:

"Kashi ɗaya cikin uku na ɗaliban da suka samu Admishin ta BECE ne suka yi rijista a makarantu."

Kwamishinan ya kara da cewa an fara gudanar da jarabawar ranar 8 ga watan Nuwamba, kuma za'a ƙarƙareta ne ranar 15 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Nasrun minallah: Dakarun Sojoji sun tarwatsa mayakan Boko Haram/ISWAP a kan hanyar Maiduguri

Ya tabbatar da cewa gwajin da za'a sake shirya musu a gaba ne zai tabbatar da cancantar su na shiga JSS1, JSS2 l, SS1 da kuma SS2.

A wani labarin kuma Kotu ta hana wanda ake zargi da yiwa Gwamna Ganduje batanci rubutu a Facebook

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta gurfanar da mutumin gaban kotu ne bisa zarginsa da batanci ga Ganduje a shafin sadarwa na Facebook

Rahoto ya nuna cewa ana zargin mutumin da kiran gwamna Ganduje da wasu daga cikin iyalansa Barayi ba tare da hujja ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel