Dubun wasu tsagerun yan bindiga da suka addabi jihohin Sokoto da Zamfara ya cika

Dubun wasu tsagerun yan bindiga da suka addabi jihohin Sokoto da Zamfara ya cika

  • Wasu mutum hudu da ake zargin manyan tsagerun yan bindiga ne sun shiga hannu a jihar Sokoto
  • Kwamandan rundunar NSCDC yace an gayyaci wani babban mutum wanda ake zargin yana da alaka da ɗaya daga cikin waɗanda aka kama
  • Rahoto ya tabbatar da cewa daga cikin mutanen da suka shiga hannu akwai yan leken asirin yan bindiga

Sokoto- Haukumar tsaro (NSCDC), ranar Laraba, ta sanar da kame wasu tsagerun yan bindiga guda huɗu a jihar Sokoto.

Channelst tv ta ruwaito cewa waɗan da ake zargin mambobin manyan ƙungiyoyin yan bindiga ne da suka addabi jihohin Sokoto da Zamfara.

Hukumar NSCDC
Dubun wasu tsagerun yan bindiga da suka addabi jihohin Sokoto da Zamfara ya cika Hoto: vangaurdngr.com
Asali: UGC

Jami'ai sun damke mutanen ne bisa zargin hannu a garkuwa da manyan mutane, fashi da makami, satar dabbobi da kuma kashe mutane a wasu yankunan waɗan nan jihohi biyu.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Miyagun yan bindiga sun kai wani mummunan hari Kaduna, sun kashe mutane

An gayyaci wani babban mutum

Kwamandan jami'an NSCDC reshen jihar Sokoto, Mohammed Saleh-Dada, yace wasu daga cikin mutanen da aka damke yan leken asirin yan bindiga ne.

A cewar kwamandan hukumarsu ta gayyaci wani babban mutum da ake zargin yana da alaƙa da ɗaya daga cikin mutanen da aka kame.

Yace:

"Mun gayyaci wani sanannen mutum a yankin karamar hukumar Dange/Shuni, jihar Sokoto, bisa zargin yana da wata alaƙa da mutum daya da ake zargi."

Mahara sun kai sabon hari Kaduna

A wani labarin kuma Miyagun yan bindiga sun kai wani mummunan hari Kaduna, sun kashe mutane

Wasu yan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun hallaka mutum 8 a wani sabon hari da suka kai kauyukan karamar hukumar Zangon Kataf, jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Kotu ta hana wanda ake zargi da yiwa Gwamna Ganduje batanci rubutu a Facebook

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa kauyukan da harin ya shafa sun haɗa da Kibori da kuma Atagjah, a karkashin yankin Aytap a kudancin jahar Kaduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel