Wajibi mu kare dukiyoyi da rayuwar mutanen Abuja, Yan majalisa sun gayyaci Ministan Buhari

Wajibi mu kare dukiyoyi da rayuwar mutanen Abuja, Yan majalisa sun gayyaci Ministan Buhari

  • Yan majalisar wakilan tarayya sun aike da katin gayyata ga ministan Babban birnin tarayya, Mohammed Adamu
  • A cewar yan majalisan wajibi ne su ɗauki matakin kare mutane da dukiyoyinsu a Abuja yayin da matsaloli ke kara yawa
  • A yan makonnin nan dai, yan bindiga na cigaba da kai hari wasu yankuna a Abuja, inda har suka sace wasu malamai a UNIABUJA

Abuja - Majalisar wakilan tarayya ta gayyaci ministan Abuja, Muhammed Bello, ya bayyana gabanta kan matsalar tsaron babban birnin tarayya Abuja.

Majalisa ta ɗauki wannan matakin ne bayan amincewa da kudirin gaggawa wanda Toby Okechukwu, mataimakin shugaban marasa rinjaye, ya gabatar.

The Cable ta rahoto cewa babban birnin tarayya Abuja, ya faɗa cikin ƙalubalen ayyukan yan bindiga a cikin yan makonnin nan.

Kara karanta wannan

Abuja: Maciji ya sari ɗan babban limami a daji bayan ya tsere daga hannun masu garkuwa

Muhammed Adamu
Wajibi mu kare dukuyoyi da rayuwar mutanen Abuja, Yan majalisa sun gayyaci Ministan Buhari Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake jagorantar muhawara kan kudirin, Okechukwu, ya shaida wa takwarorinsa cewa wajibi majalisa ta tashi tsaye wajen kare rayuka da dukiyoyin al'ummar Abuja.

Abuja ba ta taba shiga cikin wannan yanayin ba

A jawabinsa, ɗan majalisan yace:

"Abuja ba ta taba shiga cikin rashin tsaro kamar yanzu ba, daga cikin su akwai ayyukan yan bindiga da sauran manyan laifuka."
"Babu kayan tsaro na zamani a cikin Abuja, kuma waɗan da ake da su ma, ba su samun kulawan da ya kamata."
"Abun damuwa ne sosai yadda birnin ba ya samun kulawa, babu tsayayyun kayan aikin da za'a kare mutanen dake zaune a ciki."

Ɗan majalisan ya kuma zargi jagorancin babban birnin tarayya da baiwa waɗan da ba su dace ba filaye, wanda hakan watsi ne da tsarin FCT Master Plan.

Kara karanta wannan

Namiji da raino: Wani magidanci ya lakadawa diyarsa duka har Lahira saboda ya kasa lallashinta

"Abun damuwa ne yadda ake tafiyar da abubuwan da suka gama amfani a Abuja, wanda ya haɗa da mataccen abu duk da makudan kuɗin da minista yace an ware wa bangaren."

Ba tare da wani jayayya ba kowa ya amince da kudirin bayan kakakin majalisa ya bada damar tofa albarkacin baki, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Mamban majalisa ya koma APC

A wani labarin kuma Dan majalisar tarayya ya fice daga jam'iyyar hamayya, ya koma APC mai mulki

Kakakin majaisar wakilai, Femi Gbajabiamila, shine ya sanar da sauya shekar Ajao Adejumo, daga ADP zuwa APC.

Guguwar sauya sheƙa ta yi gaba da yan majalisan wakilai 20 zuwa APC cikin watanni 11 kacal, mafi yawa daga PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262