Tsohon Sarkin Kano Sanusi II ya koma makaranta karo ilmi, ya fara Digiri a Jami’ar Landan

Tsohon Sarkin Kano Sanusi II ya koma makaranta karo ilmi, ya fara Digiri a Jami’ar Landan

  • Tsohon sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II ya fara karatunsa na PhD a wata jami’ar Landan.
  • Muhammadu Sanusi II yana karantun digirdigir a wannan jami’a, har ya koma zama a kasar wajen.
  • Tun shekarar 1981 Sanusi II ya kammala digirinsa na farko a ilmin tattalin arziki a jami’ar ABU Zaria.

London - Tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya koma aji domin ya kara ilmi, inda yake karantar ilmin shari’a a wata jami’a a kasar Birtaniya.

Jaridar Premium Times ta fitar da rahoto a ranar Litinin, 8 ga watan Nuwamba, 2021, ta bayyana cewa Mai martaba Muhammadu Sanusi II ya koma aji.

Tsohon basaraken yana karatun digiri na uku watau PhD a shari’a a jami’ar Landan, kasar Birtaniya.

Muhammadu Sanusi II ya bayyana wannan da kansa a lokacin da ya zanta da Premium Times, har ya bayyana cewa yanzu ya koma Landan da zama.

Read also

Allah ya yiwa Farfesa Shehu Dalhatu na Jami'ar BUK rasuwa

Alakar tsohon Sarkin Kano da kasar Ingila

Sanusi II wanda ya yi gwamnan babban bankin Najeriya na CBN tsakanin 2009 da 2014 yana karatun PhD a lokacin da yake koyarwa a jami’ar Oxford.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bayan an sauke Malam Sanusi II daga kujerar sarautar Kano, sai ya samu aiki a matsayin mai koyarwa na musamman a jami’ar nan ta Oxford a Ingila.

University of London Hoto: uniacco.com
Sanusi II ya na karatu a jami'ar Landan Hoto: uniacco.com
Source: UGC

Bayan ‘yan watanni da jin wannan labari, sai kuma aka ji cewa masanin tattalin arzikin ya na karantar ilmin shari’a a wannan jami’a mai tsohon tarihi.

Ba wannan ne karon farko da Sanusi II ya yi alaka da makarantun Landan ba. A 2019 ne makarantar nan ta SOAS ta ba shi digir-digir na girmamawa.

Tarihin karatun Muhammadu Sanusi II

Wannan digiri na lambar yabo bai isa tsohon Sarki Sanusi II ba, ya dawo ya samu ilmi a bangaren shari’a, bayan karantun da ya yi a wasu fannonin zamani.

Read also

Buhari ya yi tafiya, Osinbajo ya jagoranci FEC, an amince a kashe N47bn a kan wasu ayyuka

Tun a 1981 Sanusi ya kammala digiri a harkar tattalin arziki a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria. A nan kuma ya yi digirgir har ya fara koyarwa a jami’ar.

Bugu da kari a 1997 ya yi digirgir a kasar Sudan, wannan karo a fannin addinin fikihun musulunci.

An kara kudin jami'ar UNIMED

Kuna da labari cewa jam’iyyar PDP ta caccaki Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu a kan kara kudin Jami’ar koyar da aikin likitanci na UNIMED da ke jihar.

PDP tace a dalilin irin wannan aiki na Gwamnatin APC, ana yawan rufe makarantun gaba da sakandare saboda zanga-zangar tsadar kudin karatu a Ondo.

Source: Legit.ng

Online view pixel