Gwamnan Neja ya gano hanyar dakile 'yan bindiga, za a kakabawa makiyaya haraji
- Gwamnan jihar Neja ya bayyana cewa, ya tsara sabbin hanyoyin magance matsalar tsaro a jiharsa da ke fama da 'yan bindiga
- Ya ce gwamnatinsa za ta dawo da shirin karbar harajai daga hannun makiyaya shanu a jihar wanda aka fi sani Dogali a shekarun baya
- Ya kuma bayyana yadda lamurran tsaro suka yi sauki a jihar cikin 'yan kwanakin nan, tare da yabawa jami'an tsaron da suka yi kokari
Neja - Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya bayyana cewa za a dawo da tsarin karbar harajin shanu da aka fi sani da “Dogali” a jihar domin yaki da ‘yan bindiga da satar shanu a jihar, Leadership ta ruwaito.
Gwamnan jihar ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Minna ranar Alhamis 4 ga watan Nuwamba.
Ya ce matakin zai kuma baiwa gwamnati damar samun bayanan da ake bukata kan adadin shanu da kuma zirga-zirgarsu a cikin jihar.
A cewarsa:
“Mun bullo da sabbin dabarun duba ayyukan ‘yan bindiga da barayin shanu a jihar wanda ba zan bayyana a nan ba. Sai dai ina shaida muku cewa, mun yi wani taron tsaro da aka fadada kwanan nan inda muka yanke shawarar bullo da harajin shanu da aka fi sani da Dogali."
Ya kara da cewa, za a karfafa cibiyoyin gargajiya a jihar yayin da kwamitin sarakunan jihar karkashin jagorancin Etsu Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar zai tabbatar da samun nasarar aiwatar da sabbin manufofin.
Ya ce barnar Boko Haram da ‘yan bindiga da sauran miyagun ayyuka sun ragu matuka a jihar saboda hadin kai da jami’an tsaro ke samu.
Ya ce al’amuran tsaro gaba daya sun samu sauki sakamakon sabon salon hadin gwiwa tsakanin jami’an tsaro da ke yaki da ‘yan ta’adda, yayin da hare-haren ‘yan ta’adda su ma suka ragu sai dai a ketare.
Gwamnan ya kara da cewa, satar shanun ma ya ragu saboda an toshe hanyoyin da suke satar shanu.
Ya kuma yabawa jami'an tsaro da suka yi abin da ake tsammani tare da jajanta cewa wasu daga cikinsu sun rasa rayukansu.
Ba wannan ne karo na farko ba da gwamnan ya bayyana bukatar dawo da harajin shanu, yayi makamancin wannan a watan Yuni a wata ziyarar da ya kai wa Sarkin Kagara a karamar hukumar Rafi, Tribune Nigeria ta ruwaito.
Rahoto: Yadda yaro karami cikin 'yan ta'addan ISWAP ya hallaka sojojin Najeriya
A wani labarin, Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, kungiyar ta'addanci ta ISIS ta fitar da wani faifan bidiyo da ke nuna wani yaro cikin 'yan ta'addan yana kashe wasu sojojin Najeriya biyu.
A cikin gajeren faifan bidiyon, an nuna wani karamin yaro wanda dan kungiyar ISWAP ne bijararren yankin kungiyar Boko Haram da ya balle, yana aiwatar da hukuncin kisa ga sojojin da aka kama a Arewa maso Gabas.
Yaron ya harbe sojojin ne da bindiga kirar AK-47.
Asali: Legit.ng