Shin dagaske kasurgumin dan bindigan da ya addabi Arewa, Dogo Gide, ya mutu? Gaskiyar abinda ke faruwa

Shin dagaske kasurgumin dan bindigan da ya addabi Arewa, Dogo Gide, ya mutu? Gaskiyar abinda ke faruwa

  • Rahotanni sun mamaye kafafen watsa labarai cewa kasurgumin ɗan bindigan nan, Dogo Gide, ya bakunci lahira
  • A cewar labaran da ake yaɗawa mataimakinsa ne ya bindige shi har Lahira, to amma shin dagaske haka ta faru?
  • Bincike daga masana da kuma masu rubutu a kan al'amuran yan bindiga a Arewa ta yamma ya tabbatar da abinda ke faruwa

Zamfara - Rahotanni na ta yawo a kafafen watsa labarai cewa ƙasurgumin ɗan bindigan nan, Dogo Giɗe, ya mutu ta hannun mataimakinsa, Sani San Makama.

Jaridar PRNigeria ta ruwaito cewa mataimakinsa ya sheƙe shi ranar Lahadi da ta gabata.

Gide, ya gawurta a fagen satar mutane da dalibai, shine ya jagoranci kitsa sace ɗaliban FGC Yauri, a jihar Kebbi a watan Yunin da ya shuɗe.

Dogo Gide
Shin dagaske kasurgumin dan bindigan da ya addabi Arewa, Dogo Gide, ya mutu? Gaskiyar abinda ke faruwa Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Waye Dogo Gide?

Kara karanta wannan

Bayan harin masallaci, yan Bijilanti sun kashe mutum 9, sun ƙona gidaje a wata rugar Fulani a jihar Neja

Ainihin sunansa shine, Abubakar Abdullahi, kuma ɗan asalin ƙaramar hukumar Maru ne a jihar Zamfara, amma ainihin ƙauyen su babu wanda ya sani.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya fara ayyukan ta'addanci ne a dajin Kuyambana, inda yake kai hari ƙauyukan dake iyakar jihohin Kaduna, Kebbi da Neja.

Ya yi ƙaurin suna wajen garkuwa da mutane domin neman kudin fansa, satar dabbobi da kuma keta haddin mata.

Dogo Gide ya fito kowa ya sansa ne a shekarar 2018, lokacin da ya sheƙe mai gidansa, Buharin Daji. Kuma ya kashe wani jagoran yan bindiga, Damina, kwanan nan.

Wani masanin tarihi kuma mai bincike kan yan bindiga a Arewa maso yamma, Murtala Ahmed Rufa'i, yace Gide yana da karfin dukiya da kuma mutane da zai mallaki manyan makamai.

Rufa'i yace:

"Dukkan ƙungiyoyin yan bindiga (Gide da sauransu) suna da binidgu ƙirar AK-47 ko AƘ-49 sama da 500. Manyan ƙungiyoyin kamar na Gide, Mai Anguwa da Turji, suna da manyan makamai kamar RPGGS da bindigar kaɓo jirgi."

Kara karanta wannan

A yi wa yan bindiga Afuwa kuma a ware kuɗaɗen ɗaukar nauyinsu, Sheikh Gumi ya magantu

Shin dagaske ne Dogo Gide ya mutu?

Duk da rahotanni da ake ta yaɗawa a kafafen watsa labarai, har yanzun babu tabbacin cewa Dogo Gide ya bakunci Lahira.

Majiyoyi da dama waɗan da ke da ilimi kan halin da yan bindiga ke ciki a Arewa ta yamma, sun shaida wa Premium Times cewa Gide yana nan a raye.

Ahmed Rufa'i ya maida martani kan wannan rahoton na mutuwar Gide da cewa, "Furofagandar sojoji ce kawai."

Wani tsohon ɗan jarida da ya yi aiki da HumAngle, Yusuf Anka, wanda ya jima yana rubutu kan yan bindiga a Arewa ta Yamma, ya musanta labarin.

Anka ya ƙara da cewa babu wani sahihin labari da ya tabbatar da mutuwar Gide, yace:

"Majiyar da nake da ita a yankin ya tabbatar mun cewa Gide yana nan da ransa. Labarin yana kafafen watsa labarai amma da na bincika sai na gano ba gaskiya bane."

Kara karanta wannan

Rikicin APC: Gwamnan APC ya bayyana rawar da ya taka wajen tsige kakakin majalisar dokokin Filato

"Giɗe yaje Ƙauyen Babbar Doka ranar Jumu'a, kuma ya shafe dogon lokaci a can, kafin ya fice da misalin ƙarfe 6:30 na yamma. Kuma ya koma ƙauyen ranar Lahaɗi da karfe 1:00 na rana, wannan shine kaɗai abinda na sani."

Wani ɗan fafutukar kare haƙƙin ɗan adam, karkashin kungiyarsu, Rundunar Adalci a jihar Sokoto, Basharu Guyawa yace duk wata majiya da yake da ita ta ƙaryata labarin.

"Zamu fi kowa farin ciki idan akace Dogo Gide ya mutu, amma a halin yanzu, ba zamu iya tabbatar da cewa an kashe shi ba."

Shin yan sanda sun samu labarin mutuwar Gide?

Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Zamfara, Mohammed Shehu, yace ba shi da masaniya kan wannan labarin amma zai tuntuɓi majiyarsa.

Bayan haka, Shehu ya bayyana cewa bai samu sahihin bayani a kan lamarin ba, kakakin yan sandan yace:

"Abinda kuke tambaya ta akai babban lamari ne, zai ɗauki dogon lokaci amma zan sanar da ku kome ake ciki nan gaba."

Kara karanta wannan

Yadda mayakan ISWAP suka kashe jami'an yan sanda, suka kone motoci a sabon harin da suka kai Borno

An sake kai hari Katsina

A wani labarin kuma Duk da dauke sabis, Yan bindiga sun sake kai wani mummunan hari a jihar Katsina

Wasu tsagerun yan bindiga sun kai sabon hari yankin karamar hukumar Faskari dake jihar Katsina duk da matakan da gwamnati ta ɗauka.

Mazauna yankin sun tabbatar da lamarin amma har zuwa yanzun ba'a san adadin yawan mutanen da suka mutu ba yayin mummunan harin ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262