Bayan lafawar tawagar Gana a Benue, wasu muggan makasa sun fito da sabon salon kisa
- Rundunar yan sandan Benue ta ja hankalin mazauna jihar a kan wasu mutane da ba a san ko su waye ba da ke bin yan mata suna kashewa
- Hakan ya biyo bayan kisan wasu yan mata biyu da aka yi a yankin North Bank da ke Makurdi, babban birnin jihar
- Rundunar ta kuma sha alwashin ganowa tare da gurfanar da wadanda ke aikata ta'asar
Makurdi, Jihar Benue - Rundunar yan sandan Benue ta ja hankalin mazauna jihar kan wani sabon salon ta’addanci da wasu da ba’a san ko su wanene ba ke amfani da shi wajen kashe mutanen da suka shiga hannunsu.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa wannan jan hankali da ‘yan sandan suka yi baya rasa nasaba da kisan wata matashiya.
An dai tsinci gawar matashiyar ne a ranar Lahadi a kusa da tsohuwar gadar da ke sada mutum da yankin 'North Bank' na Makurdi, babbar birnin jihar.
Idan za a tuna, lamari makamancin wannan ya afku makonni biyu da suka gabata inda aka tsinci gawar wata dalibar Jami’a da ke jiran takardar tafiya bautar kasa.
Lamarin ya afku ne a wannan yankin na 'North Bank' bayan wani abokin ciniki da ba’a sani ba ya kira ta a waya don ta nuna masa kayayyakin da take siyarwa.
Tun bayan tafiyarta dai, wacce ta yi cikin gaggawa, matashiyar mai suna Joy ba ta koma gida ga mahaifiyarta ba, kuma ana tsammanin sai da suka ci zarafinta kafin a kasheta.
Da take martani kan mummunan al’amarin, kakakin yan sandan jihar, DSP Catherine Anene ta bayar da tabbacin cewa rundunar tana bibiyar muggan mutanen, jaridar The Sun ta rahoto.
Ta ce:
"An ja hankalin rundunar yan sandan jihar Benue kan wani sabon salon kisa da wasu muggan mutane ke yi inda suke yaudarar yan mata zuwa wasu wurare da ba a sani ba sannan su kashe su saboda wani dalili da su kadai suka sani.
"Rundunar na nan tana bibiyar wadannan mutane kuma za ta kama su, amma wannan zai zo da sauki ne idan aka samu hadin kan al'umma.
"Ana shawartan iyaye da magabata da su sanya idanu akan yaransu domin guje ma irin haka. Ana shawartan jama'a da su kasance masu sanya idanu kan lamuran tsaro sannan su kai rahoton duk wani mutum ko ayyukan da basu yarda da shi ba."
Yadda aka sace wata budurwa bayan kammala digiri tana jiran shiga sansanin NYSC, kuma aka kashe ta a Makurdi
A gefe guda, mun kawo a baya cewa ata budurwa yar kimanin shekara 24 wacce ta kammala karatun jarida a jami'ai jihar Benuwai, Joy Onoh, ta rasa ranta hannun wasu da ba'a gano su waye ba.
Dailytrust ta ruwaito cewa matashiyar ta rasa ranta ne a wani wuri da ake kira 'North Bank suburb' dake Makurdi, babban birnin jihar Benuwai.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu mutane sun sace Joy ne bayan sun bukaci ta kai musu abubuwan da take siyarwa.
Asali: Legit.ng