Fetur ya fara wahala a Garuruwa yayin da Disamba ya karaso, masu motoci sun koma layin mai

Fetur ya fara wahala a Garuruwa yayin da Disamba ya karaso, masu motoci sun koma layin mai

  • Mazauna sun fara kokawa da karancin man fetur a babban birnin tarayya Abuja da wasu garuruwa.
  • A irinsu Abuja, Nasarawa, Taraba da Kaduna, ‘yan bumburutu sun dawo gefen hanya, suna ta yin ciniki.
  • Ana zargin masu dakon mai ne suka kara kudin mota, sai hakan ya jawo karancin fetur a gidajen mai.

Nigeria - ‘Yan bumburutu sun dawo tituna a wasu garuruwan Najeriya a sakamakon wahalar man fetur da aka fara yi a ‘yan kwanakin baya-bayan nan.

Jaridar Punch ta fitar da rahoto cewa an rufe gidajen mai da dama a Abuja, wanda dole hakan ya jawo jama’a suna sayen fetur a hannun masu bumburutu.

Rahotanni sun ce man da ake kawowa ya janye, hakan ya sa tun a karshen makon jiya ake ta layi.

Kara karanta wannan

Bincika Gaskiya: Shin hukumar 'yan sanda ta dawo da Abba Kyari bakin aiki bayan bincike?

A babban birnin tarayya Abuja, an ga dogayen layi a gidajen man da ke titin Kubwa zuwa Zuba. Kuma haka lamarin yake a wasu jihohin a halin yanzu.

Daily Post tace ana fama da wahalar fetur da dogon layi a gidajen mai a yankunan jihar Taraba. Ana saida lita a bumburutu yanzu a kan N270 zuwa N300.

Fetur ya fara wahala
Lokacin da aka yi wahalar fetur a Abuja Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Farashi ya fara canzawa

A Abuja, ‘Yan bumburutu na saida galan mai cin lita goma a kan N2, 000 zuwa N2, 500 ga wadanda ba su iya tsayawa su bi dogon layi a gidan mai.

A garin Zaria wani wanda ya sha man bumburutu ya shaidawa Legit.ng Hausa cewa ana saida galan mai cin lita biyar tsakanin N1, 000 zuwa N1, 200 a jiya.

Abin da ‘yan kasuwa suke cewa

Wani babban jami’in kungiyar IPMAN ta ‘yan kasuwan mai na kasa ya shaidawa manema labarai cewa masu tankokin mai ne suke jawo wahalar da ake yi.

Kara karanta wannan

Dinbin mutane sun makale carko-carko yayin da gini mai hawa 20 ya ruguje a Najeriya

“Watakila ayi wahalar fetur saboda an samu karancin shigowar mai. Sannan masu tankoki sun kara farashin dako, ba a san dalili ba.” – Jami’in IPMAN.

Mai magana da yawun bakin IPMAN, Ukadike Chinedu, yace ba su da hannu wajen boye mai.

Abin da mutane suke tsoro shi ne za a bukaci fetur sosai yayin da bukuwan kirismeti da sabuwar shekara suka karaso, domin ana yawan yin tafiye-tafiye.

Dangote Cement PLC ya ci kazamar riba

A makon nan ne aka ji cewa kudin da kamfanin simintin Dangote PLC ya samu a cikin watanni tara da suka wuce shekarar 2021 ya zarce Naira tiriliyan daya.

Duk nahiyar Afrika babu babban kamfanin siminti irin Dangote Cement Plc. Daga cikin abin da ya sa aka samu kazamar riba shi ne an fara yin tituna da siminti.

Asali: Legit.ng

Online view pixel