Zan nemi kujerar Malam El-Rufa'i a zaɓen 2023 karkashin PDP, Sanata Shehu Sani
- Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya bayyana shirinsa na tsayawa takarar gwamnan jihar Kaduna karkashin PDP
- Shehu Sani, wanda tsohon ɗan jam'iyyar PRP ne, ya tabbatar da komawarsa PDP a hukumance ranar gangamin jam'iyya na ƙasa
- A cewarsa mutane ne suka matsa masa ya nemi takarar, kuma zai nemi kujerar da zai canza abinda aka ɓata
Kaduna - Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani, yace zai nemi kujerar gwamnan jihar Kaduna karkashin inuwan jam'iyyar PDP a babban zaɓen 2023.
BBC Hausa ta rahoto cewa tsohon ɗan majalisar dattijai ya jima da ficewa daga jam'iyyar PRP, wacce ya nemi zarcewa kujerar sanata a shekarar 2019 amma bai bayyana inda ya koma ba.
Sai dai a ranar Asabar da PDP ta gudanar da gangamin taron ta na ƙasa, an hangi Shehu Sani ya halarci taron, hakan ya tabbatar da ya koma jam'iyyar.
Rade-Radin sauya sheka zuwa APC: An gano babban dalilin da ya hana Goodluck Jonathan halartan gangamin PDP
Meyasa zai nemi takarar gwamnan Kaduna?
Shehu Sani ya shaida wa manema labarai cewa ba bisa ra'ayin kansa ne zai tsaya takarar gwamnan ba, mutane ne suka nemi ya yi hakan.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Tsohon ɗan majalisar yace:
"Mutane ne suka bukaci mu tsaya takara, kuma gara mu nemi kujerar da zamu iya kawo canjin da ake buƙata. Takarar gwamna zan nema."
"Hakanan kuma gani na da kuka yi yau a wurin wannan taron na nufin na koma jam'iyyar PDP a hukumance."
A wani labarin kuma Gwamna Lalong na jihar Filato yace yasan radadin tsige mutum daga mukamin shugaban majalisa
Gwamnan ya kuma musanta jita-jitar da ake yaɗa wa cewa shine ya haɗa komai ya bada umarnin cire kakakin majalisar dokokin Filato.
Gwamnan yace ɓangaren majlisa zaman kansa yake, kuma suna tafiyar da harkokinsu ba tare da jiran umarnin wani ba.
Asali: Legit.ng