Yan bindiga sun kashe aƙalla mutum 5 a wani sabon hari da suka kai jihar Katsina
- Wasu miyagun yan bindiga sun sake kai sabon hari Kauyen Dangeza a karamar hukumar Batsari dake jihar Katsina
- Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun hallaka mutum biyar yayin da wasu da dama suke asibiti domin kula da lafiyarsu bayan harin
- Karamar hukumar Batsari na cikin yankunan da hare-haren yan bindiga ya fi kamari a jihar Katsina
Katsina - Premium times ta ruwaito cewa adadi mai yawa na tsagerun yan bindiga sun farmaki ƙauye Dangeza a jihar Katsina kuma sun kashe mutum 5.
Dangeza, na ɗaya daga cikin kauyukan dake ɗauke da manoma da yan kasuwa a ƙaramar hukumar Batsari, inda suke fama da yawaitar harin yan bindiga.
Ko a kwanan nan, hakimin Batsari, kuma sarkin Ruman Katsina, Tukur Muazu, yace yan bindigan dake tserowa daga ruwan wutan sojoji a Zamfara sun fara mamaye yankin.
Yadda tsagerun suka kai sabon harin
Da yake zantawa da manema labarai, ɗaya daga cikin mazauna yankin, Jamilu Ali, yace yan bindigan sun farmaki ƙauyen ne ranar Alhamis da safe.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yace:
"Yan bindigan sun zo da sanyin safiya, lokacin da mazauna ƙauyen suke shirin fita kasuwar mako a garin Batsari."
"Mafi yawan waɗan da maharan suka kashe yan fitar safiya ne, dake son hawa motar farko dake yin sammako."
Mutum nawa harin ya shafa?
A cewarsa harin ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 5, yayinda wasu adadi mai yawa na mutanen suke kwance a asibiti a Batsari.
Jamilu ya ƙara da cewa duk da ƙoƙarin da yan Bijilantin ƙauyen suka yi, amma sai da maharan suka saci kayayyakin da mazauna ƙauyen suka siyo.
Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Katsina, Gambo Isa, bai ɗaga kiran salula da aka masa ba domin tsokaci kan lamarin.
A wani labarin kuma Bayan harin masallaci, Yan Banga sun hallaka Hakimi da ɗan uwansa a jihar Neja
Wasu yan banga sun ɗauki fansa kan harin da aka kai masallaci a jihar Neja, inda aka kashe mutane tare da sace wasu.
Rahoto ya nuna cewa yan bangan sun hallaka wani hakimi da ɗan uwansa bisa zarginsu da hannu a harin masallaci.
Asali: Legit.ng