Dana ba zai ci amanarki ba saboda kina da kyau da shafaffen tumbi – Tsohon gwamna ga surukarsa
- Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose, ya yaba tare da alfahari da irin kyawun sura da Allah ya yiwa matar dansa
- Fasoye ya ba amaryar tabbacin cewa dansa ba zai ci amanarta ba saboda tana da kyau, shafaffen tumbi da kuma fararen hakora
- Ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabin uban ango wanda yake wajibi a al'adar Yarbawa
Jihar Lagos - Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose, ya ce dansa bai da wani dalili na cin amanar amaryarsa saboda tana da kyau da shafaffen tumbi da kuma fararen hakora.
Fayose ya yi magana ne a cikin wani bidiyon bikin wanda ya bayyana kuma ya shahara a ranar Talata.
A cikin bidiyon, yayin da yake bayar da jawabin uban ango, wanda yake wajibi bisa al'adar Yarbawa, Fayose ya ce kyawun mace yana taka muhimmiyar rawar gani wajen daidaita aure.
Ya kuma ce mazajen da basu da kyawawan mata "suna karewa da cin amanar aurensu", jaridar The Cable ta rahoto.
Ya ce:
"Duk wanda ya gan ki a yau zai ga cewa nayi sa'a dana yana auren kyakkyawa. Idan mutum bai da kyakkyawar mace, zai kare da cin amanar auren. Dana bai da wani dalili na cin amana. Kina da kyau, da shafaffen tumbi, fararen hakora, kina da komai ya ji."
Ya kuma yi wa ma'auratan addu'a yayin da ya shawarci dansa da ya gina gadonsa daga sunan mahaifinsa.
An yi bikin auren tsakanin Oluwanigba Fayose da Olamide Adekunle Abdul a dakin taro na fadar sarki, Lekki Peninsula II, Lagos, a ranar Asabar.
Manyan mutanen da suka halarci bikin sun hada da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike; gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi; gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde da sauransu.
Ga bidiyon wanda shafin goldmynetv ya wallafa a Instagram:
Soyayya dadi: Yadda gimbiya ta bar masarauta da makudan miliyoyi ta auri talaka tukuf
A wani labarin, Gimbiya Mako ta kasar Japan ta fice daga gidan sarauta kuma ta auri saurayinta talaka mai suna Kei Komuro, inda ta bar kambunta na sarauta saboda soyayya.
Matashiyar mai shekaru 30 ta yi tattaki tare da masoyinta da suka hadu a jami'a a Tokyo ranar Talata, wanda ya kawo karshen zaman da suka yi na tsawon shekaru takwas zuwa zaman aure.
An tilastawa Mako barin kambun sarautarta kamar yadda al'adun Japan suka tsara game da auren talakawa.
Asali: Legit.ng