‘Yan bindiga sun saki ‘yan asalin jihar Benue da suka sace a Zamfara
- Yan bautar kasa guda biyu da wasu ‘yan asalin jihar Benue da aka yi garkuwa da su kwanan nan a jihar Zamfara sun samu ‘yanci
- Wadanda lamarin ya cika da su sun kubuta ne bayan shafe tsawon kwanaki 13 a hannun 'yan bindiga
- An tattaro cewa kokarin hadin gwiwa tsakanin Gwamna Samuel Ortom da hukumomin Benue Links da kuma iyalan wadanda abin ya shafa ne ya kai ga kubutar su
Benue - Wasu 'yan asalin jihar Benue, ciki harda masu yiwa kasa hidima biyu da aka sace a karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara yayin da suke cikin tafiya sun samu yanci.
Daily Trust ta rahoto cewa yan bautar kasa biyu, Jennifer Awashima Iorliam da Joseph Zakaa na a hanyarsu ta zuwa sansanin NYSC a jihar Kebbi lokacin faruwar lamarin.
Sauran wadanda suka samu yanci sune Sedoo Kondo, wani dalibin jami'ar Usman Dan Fodio, Sokoto, wanda ke a hanyarsa ta zuwa makaranta, Ruth Sesuur Tsokar, wacce ta ziyarci wasu yan uwanta a Kebbi.
Sai kuma wasu 'yan uwan juna biyu, Muhammadu Saminu da Safiam Muhammadu, wadanda ke a hanyarsu ta zuwa jihar Sokoto.
Jaridar ta kuma rahoto cewa wadanda lamarin ya rutsa da su suna tafiya ne a cikin wata motar Benue Links wanda suka tashi daga Makurdi kafin aka sace su tsawon kwanaki 13 da suka gabata.
Wata yar uwan daya daga cikin mutanen da aka saki, Judith Iorliam, ta fada ma manema labarai a Makurdi a ranar Laraba cewa an sake su ne misalin karfe 6:00 na yammacin ranar Talata.
Ta ce:
"Eh, an sake su a jiya (Talata) da misalin karfe 6:00 na yamma."
Daily Post ta rahoto cewa an hada hannu ne tsakanin Gwamna Samuel Ortom da hukumomin Benue Links da kuma iyalan wadanda abin ya shafa wajen sako su.
An shiga halin fargaba a sansanin NYSC da ke Zamfara yayin da ‘yan bindiga suka sace masu yiwa kasa hidima
A baya Legit.ng ta rahoto cewa, Yan bautar kasa sun shiga zullumi a jihar Zamfara biyo bayan sace wasu takwarorinsu da ‘yan bindiga suka yi a hanyarsu ta zuwa sansanin NYSC da ke karamar hukumar Tsafe.
Koda yake rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da sace yan bautar kasar biyu a hanyar babban titin Sheme-Tsafe da ke jihar, shaidu sun ce har yanzu ba a ga wasu mutum shida ba bayan afkuwar lamarin a ranar Talata.
Rundunar ‘yan sandan ta ce an kaddamar da aikin bincike da ceto domin kubutar da yan bautar kasar da sauran mutanen da lamarin ya cika da su.
Asali: Legit.ng