Sheikh Gumi: Za a yi nadamar ayyana 'yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda

Sheikh Gumi: Za a yi nadamar ayyana 'yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda

  • Sheikh Ahmad Gumi ya gargadi gwamnatin tarayya game da ayyana 'yan bindiga 'yan ta'adda
  • A baya-bayan nan dai daidaikun mutane da kungiyoyi suna ta kira ga gwamnati ta ayyana 'yan bindigan 'yan ta'adda
  • Gumi ya ce hakan abu ne mai hatsari domin zai bawa kungiyoyin kasashen waje masu da'awar jihadi gindin zama sannan matasa marasa aiki za su shiga

Kaduna - Shiekh Ahmad Gumi, fitaccen malamin addinin musulunci ya ce masu ikirarin yin jihadi daga kasashen waje na iya shigowa Nigeria idan aka ayyana 'yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda.

Tun da baya, malamin ya taba rokon gwamnatin tarayya ta yi wa 'yan bindigan afuwa sannan ta basu tallafi don sauya halayensu su kama sana'a.

Sheikh Gumi: Za a yi nadamar ayyana 'yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda
Za a yi nadamar ayyana 'yan bindiga a matsayin 'yan ta'adda, Sheikh Gumi. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Tsoro da zaman dardar: Yadda shirin NYSC ya zama abin tsaro ga 'yan bautar kasa

Da ya ke tsokaci kan kiraye-kirayen da ake yi a baya-bayan nan na neman a ayyana 'yan bindiga a matsayin yan ta'adda, Gumi, cikin sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, akwai abubuwa masu hatsari da ka iya biyo baya.

Malamin ya ce makalawa 'yan bindigan lakanin ta'addanci zai janyo matasa marasa aikin yi su yi sha'awar shiga harkar ta 'yan bindiga.

Wani sashi na sanarwar ta ce:

"Barnar da yan bindiga ke yi a arewa maso yamma tsawon lokaci ya fara zama ta'addanci domin duk lokacin da aka kashe wadanda ba su ji ba basu gani ba, hakan ta'addanci ne."

Ya cigaba da cewa a zamanin yanzu gaskiya ta zama abin za a iya kallon ta daga bangarori daban-daban inda ya bada misalin yadda wasu yan banga ke halaka fulani kawai don su yi kama da makiyaya hakan ke saka yan bindigan kai hari a kauyuka don daukan fansa.

Kara karanta wannan

Majalisa za ta mika ƙudurin ayyana 'yan bindiga da 'yan ta'adda gaban fadar shugaban kasa

"Sa'an da aka yi kan 'yan bindigan shine fulani ne suka fi sha'awan shiga cikinsu domin yadda aka kabilantar da abin. Amma da an ayyana su yan ta'adda - musamman 'yan ta'adda musulmi, kungiyoyin kasar waje masu da'awar jihadi za su hada kai da su.
"Sannan matasa marasa aikin yi za su yi sha'awar shiga. Fadin 'Allahu Akbar' da AK-47 yayin da ake tunkarar al'umma da ke rayuwa karkashin gwamnati wacce ba ta musulunci ba abu ne da ke jan hankalin masu tsatsauran ra'ayi - tuni, kungiyoyin ta'addanci sun fara kokarin jan hankalin matasan mu." - Sheikh Ahmad Gumi

Sokoto: Yadda ƴan bindiga suka amshe miliyoyi daga basarake kuma suka ƙi sako waɗanda suka yi garkuwa da su

A wani rahoto daga Sokoto, 'Yan bindiga sun amshe Naira miliyan 2.2 (N2,200,000) a matsayin kudin fansa amma sun ki sakin mutane 20 da su ka sata.

Kara karanta wannan

APC da PDP ba za su taba sauyawa ba: Jega ya bayyana matsalolin APC da PDP

Buzu, na biyu a hatsabibanci daga Bello Turji, duk da an biya shi makudan kudade don sakin mutane 20 da su ka sata a Gatawa ya murje ido ya lamushe kudin babu wani bayani.

Premium Times ta ruwaito yadda ‘yan bindigan su ka aika wa dagacin Burkusuma da sarkin Rafi wasika inda su ka bayyana cewa su na bukatar N20,000,000 a matsayin kudin fansar wadanda su ka sata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164