Soja ya fusata ya karya wa ma'aikaciyar jinya ƙafa yayin da ya kai matarsa asibiti haihuwa

Soja ya fusata ya karya wa ma'aikaciyar jinya ƙafa yayin da ya kai matarsa asibiti haihuwa

  • Cikin fushi, wani soja ya yi wa ma'aikaciyar jinya duka har ya karya mata kafa a asibiti a garin Ilorin
  • Hakan ya faru ne a lokacin da ya kai matarsa haihuwa amma aka bukaci ya kawo kayan haihuwa
  • Rundunar sojojin Nigeria ta tabbatar da afkuwar lamarin kuma ta ce ta tsare sojan don masa tambayoyi

Ilorin, Kwara - Wani soja daga 22 Armoured Brigade na rundunar sojojin Nigeria, Sobi Cantonment, Ilorin jihar Kwara ya yi wa ma'aikaciyar jinya duka har ya karya mata kafa daya.

Jaridar Daily Trust ta rawaito lamarin ya faru ne a karshen mako a lokacin da sojan ya kai matarsa mai juna biyu asibiti domin ta haihu.

Babban maganan: Soja ya fusata ya karya wa ma'aikaciyar jinya ƙafa yayin da ya kai matarsa asibiti haihuwa
Soja ya fusata ya karya wa ma'aikaciyar jinya ƙafa yayin da ya kai matarsa asibiti haihuwa. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Majiyoyi sun shaidawa jaridar cewa rikicin ya samo asali ne a lokacin da ma'aikaciyar jinyar ta bukaci a siya kayan haihuwa kafin a karbi matar sojan a bada gado a dakin haihuwa.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar: An tura mahaifi na gidan yari don ya ƙi yarda in yi makarantar boko

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Majiyar ta kara da cewa:

"A maimakon ya tafi ya kawo kayan haihuwan, sojan ya ki, ya ce gwamnatin jihar ta tanadi irin wannan kayayakin ga mata masu juna biyu da suka zo asibti haihuwa.
"Amma ma'aikaciyar jinyar ta shaidawa sojan cewa bai fahimci sakon bane, don haka, ta dage cewa sai ya kawo kayan haihuwan domin ayi amfani da su wurin taimakawa matarsa haihuwa."

Wata majiyar daban ta kara da cewa abin da ma'aikaciyar jinyar ta fada wa sojan ya bata masa rai har ta kai ya karya mata kafa guda daya.

Hakan ya yi sanadin an bawa ma'aikaciyar jinyar gado a asibiti inda a halin yanzu ta ke samun kulawar likitoci.

Da aka tuntube shi game da batun, Kakakin 22 Birgade na Rundunar Sojojin Nigeria, Sobi Cantonment, St. Sgt Wasiri ya tabbatar da afkuwar lamarin.

Kara karanta wannan

Buhari: Ba zan huta ba har sai na tabbatar Najeriya ba ta fama da kalubalen tsaro

Ya ce hukumomin rundunar ta tsare sojan domin ta yi masa tambayoyi game da lamarin.

An sha mamaki bayan gano cewa gardin namiji aka tura gidan yari na mata ba tare da an gane a kotu ba

Wani lamari mai ban mamaki ya auku a gidan gyaran halin mata da ke Shurugwu a makon da ya gabata, inda aka gano wata fursuna ba mace bace, katon namiji ne kamar yadda LIB ta ruwaito.

Praise Mpofu mai shekaru 22 ya na sanye da suturar mata ne a lokacin da aka kama shi inda ya bayyana kamar karuwa don ya yaudari maza ya yi musu sata.

An kama Mpofu ne bayan ya yi wa wani mutum da ke yankin Gweru sata. An samu rahoto akan yadda mutumin ya caskewa Mpofu kudi don su kwana tare da shi a tunanin sa mace ne, daga nan Mpofu ya yashe shi ya tsere.

Kara karanta wannan

Muna cikin tafiya sai muka ji kara - Fasinjojin jirgin da aka kai wa hari sun bayyana halin da suka shiga

Asali: Legit.ng

Online view pixel