Ba zama: Wani mutum ya yi garkuwa da dan sufeton 'yan sanda
- Jami'an tsaro sun yi nasarar cafke wani matashi da yayi garkuwa da dan wani sufeton 'yan sanda a jihar Abia
- Rundunar tsaro ta NSCDC ta ce wanda ake zargin ya je har gidan iyayen yaron ya dauke shi bayan ya yaudare shi da sunan zai siya masa biskiti
- Tuni dama ya yi cinikin yaron a kan kudi N500,000 amma sai tsoro ya kama shi, don haka ya jefar da shi ahanya
Abia - Rundunar tsaro ta NSCDC ta gurfanar da wani matashi mai suna Ifeanyi Joseph dan shekara 21, bisa zarginsa da yin garkuwa da dan wani Sufeton 'yan sanda mai shekaru hudu.
Kwamandan NSCDC, Ayinla T. Olowo ya ce an cafke wanda ake zargin ne bayan samun wasu bayanai na sirri.
Wanda ake zargin, ya dauki yaron daga gidan iyayensa da ke Laguru Ubakala, karamar hukumar Umuahia ta kudu, jaridar The Nation ta rahoto.
Olowo ya kara da cewa Joseph ya isa inda suka yi za su hadu da mai siyan yaron domin karbar N500,000 da ya bukata.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sai dai kuma yayi zargin cewa ana iya kama shi, don haka sai ya yasar da yaron sannan ya tsere.
Jami’an tsaro sun gano inda yake sannan kuma suka yi ram da shi.
Wanda ake zargin ya amsa laifinsa, inda yace ya dauki yaron ne daga gidan iyayensa bayan ya yaudare shi da cewar zai siya mai biskiti da alawa, rahoton The Eagleonline.
Dubun masu garkuwa da mutane, yan leken asiri da masu kaiwa yan bindiga kayan abinci ya cika a jihar Sokoto
A wani labarin kuma, mun ji cewa jami'ai sun damke wasu da ake zargin masu sace mutane ne da masu aikin kaiwa yan fashin daji abinci a jihar Sokoto.
Jaridar Channels Tv ta rahoto cewa hukumar tsaro ta NSCDC ce ta fitar da sanarwar samun wannan nasara ranar Litinin.
Waɗanda ake zargin suna aikata ta'asarsu ne a yankin kananan hukumomin Tureta da kuma Dange/Shuni dake kudancin Sokoto.
Asali: Legit.ng