Dubun masu garkuwa da mutane, yan leken asiri da masu kaiwa yan bindiga kayan abinci ya cika a jihar Sokoto

Dubun masu garkuwa da mutane, yan leken asiri da masu kaiwa yan bindiga kayan abinci ya cika a jihar Sokoto

  • Jami'an tsaro sun samu nasarar cafke masu garkuwa da mutane 11, yan leken asiri da kuma masu jigilar kaiwa yan bindiga abinci a Sokoto
  • Hukumar NSCDC ta bayyana cewa mutanen da ake zargin suna aikinsu ne a yankunan Tureta da Dange/Shuni
  • Kwamandan NSCDC na jihar Sokoto, yace wasu daga cikin yan bindigan da aka kame sunce N10,000 aka taɓa biyansu

Sokoto - Rahotanni sun bayyana cewa jami'ai sun damke wasu da ake zargin masu sace mutane ne da masu aikin kaiwa yan fashin daji abinci a jihar Sokoto.

Jaridar Channels Tv ta rahoto cewa hukumar tsaro ta NSCDC ce ta fitar da sanarwar samun wannan nasara ranar Litinin.

Waɗanda ake zargin suna aikata ta'asarsu ne a yankin kananan hukumomin Tureta da kuma Dange/Shuni dake kudancin Sokoto.

Read also

Yan bindiga sun kashe mutum 21 sakamakon bude wuta da suka yi a cikin kasuwa a Sokoto

Jihar Sokoto
Dubun wasu masu garkuwa da mutane 11 da masu kaiwa yan bindiga kayan abinci ya cika a jihar Sokoto Hoto: channelstv.com
Source: UGC

A cewar hukumar NSCDC, biyu daga cikin waɗanda ake zargin sun amsa laifinsu cewa da hannunsu a wasu hare-hare da aka kai kwanan nan.

Daga cikin irin waɗannan hare-haren da suka kai harda wanda aka kai kwanan nan a Lambar Tureta da Dabagi Haske, inda aka kashe mutum 8.

Jami'ai sun kama masu jigilar kayan Abinci

Hakazalika, hukumar ta bayyana cewa ana zargin wasu mutum biyu daga cikin waɗanda aka kama da aikin kaiwa yan bindiga abinci da kuma leƙen asiri.

Yayin da wasu mutum 7 suka amsa laifinsu cewa suna da hannu a sace shanu da dama a yankin kananan hukumomin Rabba da Wurno.

Wasu jami'ai ne suka damke mutanen?

Da yake bayani kan waɗanda aka kama, kwamandan NSCDC na jihar, Muhammad Saleh-Dada, yace jami'ansa sun samu wannan nasarar ne da taimakon ƙungiyar yan sa kai na ƙaramar hukumar Wurno.

Read also

Yan sakai sun hallaka limamin masallaci da wasu mutum 10 a jihar Sokoto

Kwamandan yace:

"Wasu daga cikin masu garkuwan da aka kama sun amsa cewa dasu aka kai hare-hare da dama amma N10,000 kacal aka ba su."

A wani labarin kuma kunji cewa a jihar Katsina dake makotaka da Sokoto, wasu miyagun yan bindiga sun buɗe wa masallata wuta

Dailytrust ta rahoto cewa lamarin ya auku ne lokacin da mutanen ke tsaka da sallar Magrib ba zato yan bindigan suka buɗe musu wuta, ranar Talata.

Legit.ng Hausa ta gano cewa tuni aka gudanar da jana'izar waɗanda suka rasu da safiyar ranar Laraba, yayin da waɗanda suka ji raunuka aka kaisu asibiti.

Source: Legit.ng

Online view pixel