Amurka ta bayyana taimakon da zata wa Najeriya wajen kawo ƙarshen yan bindiga

Amurka ta bayyana taimakon da zata wa Najeriya wajen kawo ƙarshen yan bindiga

  • Gwamnatin ƙasar Amurka ta sha alwashin taimakawa ƙawarta Najeriya wajen kawo karshen ayyukan yan bindiga
  • Amurka tace zata gudanar da wasu shirye-shirye da take ganin zasu taimaka matuƙa wajen kawo ƙarshen kalubalen
  • Hakanan kuma Amurka ta kore duk wasu shakku game da sabbin jiragen yaƙin da ta siyarwa Najeriya na Super Tucano

United States - Gwamnatin ƙasar Amurka tace zata taimakawa Najeriya a yaƙin da take yi da yan bindiga, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

Mataimakin mai bada shawara kan tsaro na Amurka, Jon Finer, shine ya bada wannan tabbacin a taron manema labarai a Abuja, ranar Litinin.

Jon Finer
Amurka ta bayyana taimakon da zata wa Najeriya wajen kawo ƙarshen yan bindiga Hoto: dailytrust.com
Source: UGC

A jawabinsa, Mista Finer yace:

"Zamu samar da shiri na musamman na fasaha da adalci, domin tallafawa Najeriya ta shawo kan ƙalubalen yan bindiga."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Read also

Babban dalilin da yasa yan Najeriya ba zasu amince da Igbo ya zama shugaban ƙasa a 2023 ba, Dokpesi

"Hakanan kuma zamu cigaba da kirkiro shirye-shirye makamantan irin wannan domin taimakawa ƙasa Najeriya."

Ta ya Najeriya zata yi amfani da Super Tucano?

Dangane da sabbin jiragen da Amurka ta siyarwa Najeriya ƙirar Super Tucano, da kuma tsoron yadda ƙasar zatayi amfani da su, Finer yace:

"Ina tunanin mun wuce wannan wurin mun yi bayanin tsammanin mu wajen amfani da jiragen yaƙin ta hanyar da ya dace."

Ta ya za'a kawo ƙarshen ƙungiyar yan aware IPOB?

Hakanan kuma, Finer ya ƙara da cewa tawagar wakilan gwamnatin Amurka ta tattauna da gwamnatin Najeriya game da haramtacciyar kungiyar IPOB.

A cewarsa tattaunawar ta maida hankali ne kan yadda za'a warware matsalolin da suka kirkiri ƙungiyar.

A wani labarin kuma Yan bindiga sun shiga uku yayin da Rukunin karshe na sabbin jiragen yaƙin 'Super Tucano' sun iso Najeriya

Ministan yaɗa labarai da Al'adu, Alhaji Lai Muhammed, yace sabbin jiragen 12 sun canza wasan, sojoji na cigaba da samun nasarori.

Read also

Yadda yan bindiga ke sako mutanen da suka kama ba tare da biyan kudin fansa ba a Zamfara

Ministan ya kuma yi martani kan rahoton cewa rundunar sojojin sama ta biya yan bindiga miliyan N20m don kada su harbo jirgin shugaban ƙasa.

Source: Legit

Online view pixel