'Yan bindiga sun kira wayar wani a coci, ya fito sun bindige shi sun gudu

'Yan bindiga sun kira wayar wani a coci, ya fito sun bindige shi sun gudu

  • Wasu 'yan bindiga sun harbe wani mutum yayin da yake bauta a coci a wani yankin jihar Ilorin
  • Rahoto ya bayyana cewa, a halin yanzu ana kan binciken gawa da kokarin kamo 'yan bindigan
  • A bangarori da yawa a Najeriya akan samu kashe-kashe a wuraren bauta, lamarin da ya ke kara ta'azzara rashin tsaro

Wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kashe wani wakilin kamfanin gidaje da ke Ilorin mai suna Sina Babarinde.

Babarinde, memba ne na Cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG), an harbe shi ne yayin bauta a cocin Living Word Parish da ke hanyar Basin, Ilorin, PM News ta ruwaito.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin a ranar Litinin, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kwara, Okasanmi Ajayi, ya ce lamarin ya faru ne yayin da ake gudanar bautar cocin na RCCG da misalin karfe 7 na safe.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun yi wa ‘yan sanda kwanton bauna, sun yi awon gaba da bindiga

'Yan bindiga sun kira wayar wani a coci, ya fito sun bindige shi sun gudu
Barnar da 'yan bindiga ke yi a Najeriya | Hoto: dailytrust.com
Asali: Twitter

Ya ce marigayin ya samu kiran waya, yayin da ya fita daga cocin don amsawa, sai aka ji sautin harbin bindiga. Wannan ya ja hankalin masu bauta, nan da nan suka fito don ganin abin da ke faruwa, sun sami Babarinde a kwance cikin jini.

Ajayi ya kara da cewa:

"An gano cewa an harbe shi a kai."

'Yan sanda sun fara bincike

An ajiye gawar mamacin a dakin ajiye gawarwaki na asibitin koyarwa na jami’ar Ilorin (UITH) kafin jana'iza nan gaba, Premium Times ta ruwaito.

An gano sauran harsashin da aka yi amfani da shi wajen kashe mamacin yayin da aka fara gudanar da bincike kan kisan.

An ce hukumomin tsaro na kokarin ganin an kamo wadanda suka aikata wannan aika -aikar tare da tabbatar da cewa an kiyaye lafiyar 'yan kasa.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun afka caji ofis, sun sace ƴar sanda da bindigu masu ɗimbin yawa

'Yan bindiga sun kai hari asibiti, sun bankawa motar hukumar DSS wuta

A wani labarin, Wasu 'yan bindiga da ke tafe a cikin motocin SUVs guda hudu a yau Lahadi sun kashe mutane biyu yayin wani hari a garin Nnewi mai yawan masana'antu a jihar Anambra.

Sun kuma bankawa daya daga cikin motoci mallakar hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) wuta.

Jaridar The Nation ta tattaro cewa 'yan bindigan sun kai harin ne a daidai lokacin da masu ibada ke kammala hidimarsu cocinsu daban-daban.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.