'Yan bindiga sun kai hari asibiti, sun bankawa motar hukumar DSS wuta

'Yan bindiga sun kai hari asibiti, sun bankawa motar hukumar DSS wuta

  • Wasu tsagerun 'yan bindiga sun hallaka mutane biyu a yankin Nnewi na jihar Anambra a yankin kudu maso gabas
  • Sun bankawa motar jami'an hukumar DSS wuta, sun kuma kai hari ofishin hukumar kula da haddura ta kasa (FRSC)
  • Sun kuma kai hari a asibitin koyarwa na NAUTH kafin daga suka wuce zuwa wasu yankunan jihar

Anambra - Wasu 'yan bindiga da ke tafe a cikin motocin SUVs guda hudu a yau Lahadi sun kashe mutane biyu yayin wani hari a garin Nnewi mai yawan masana'antu a jihar Anambra.

Sun kuma bankawa daya daga cikin motoci mallakar hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) wuta.

Jaridar The Nation ta tattaro cewa 'yan bindigan sun kai harin ne a daidai lokacin da masu ibada ke kammala hidimarsu cocinsu daban-daban.

Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun bankawa motar hukumar DSS wuta ta kone kurmus
'Yan bindiga | Hoto: thenationonlineng.net
Source: Twitter

Wata majiya ta ce sun hari ofishin Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) inda suka rika yin harbi akai-akai yayin da ma’aikatan ke gudu don tsira

Read also

Sanatan APC ya maida wa Sanusi martani kan ikirarin cewa tattalin Najeriya ya kusa ya ruguje

An tattaro cewa sun kuma kai hari asibitin koyarwa na Nnamdi Azikiwe NAUTH Nnewi inda suka bude wuta suka jikkata mutum daya.

Sai dai majiyar ta shaida cewa 'yan bindigar sun nuna alamar sanayya ga masu karanta jarida kyauta a unguwar da ke kusa da garin wanda a cewarsa, sun jinjina musu.

Amma wani mutumin da a cewar majiyar, wanda ya yi kokarin daukar bidiyon lamarin an harbe shi a yankin mahadar Kotun Eme, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

An kuma ce an kashe wani mutum a yankin mahadar Traffic na garin.

Daga baya ‘yan bindigar sun zagaya cikin gari, sun bi ta Nkwo Nnewi Triangle sannan suka nufi hanyar Nnobi.

An bayyana cewa sun bar garin kafin motar sulke ta Sojoji ta iso.

Read also

Yan sanda sun kame waɗanda ake zargi da kisan babban malamin Addini a jihar Kano

Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan (PPRO) Ikenga Tochukwu ya tabbatar da faruwar lamarin amma ya ce rundunar ba ta samu cikakken bayani ba.

Ya ce:

“Da misalin karfe 2 na rana, ranar 3 ga Oktoba 2021, rundunar ta samu kiran gaggawa na gobara a Nnewi. Yanzu haka jami’an ‘yan sandan suna nan a kasa kuma tuni aka killace yankin.”

COAS ga sojoji: Kada ku daga kafa wajen ragargazar 'yan ta'adda

A wani labarin, Babban hafsan sojin kasa Laftanar Janar Farouk Yahaya ya umarci runduna ta bataliya ta 4 ta musamman da ke Doma da su ci gaba da jajircewa don ganin sun kubutar da kasar daga hannun mayakan Boko Haram da sauran 'yan ta'adda a Arewa da sauran sassan kasar.

Yahaya ya ba da wannan umarnin ne a lokacin da yake zantawa da Daily Trust yayin ziyarar aiki da ya kai hedikwatar bataliyar da ke karamar Hukumar Doma ta Jihar Nasarawa don duba wasu wurare a barikin.

Read also

'Yan fashi sun afka wa coci domin sace kudi, sun daba wa mai gadi wuka a Abuja

Ya ce kalubalen tsaro da ke fuskantar kasar nan ba za a iya shawo kansu ba idan aka babu kulawa da jajircewa daga gwamnatin tarayya.

Source: Legit

Online view pixel