Labari da ɗuminsa: Gwamnatin Kogi ta naɗa sabon Attah na Igala

Labari da ɗuminsa: Gwamnatin Kogi ta naɗa sabon Attah na Igala

  • Majalisar kolin jihar Kogi ta amince da nada Prince Mathew Alhaji Opaluwa a matsayin Attah na Igala
  • Majalisar ta amince da nadin sabon basaraken ne yayin taronta karo na 6 da ta gudanar a ranar Litinin a Lokoja
  • Kafin nadinsa, Prince Mathew Alhaji Opaluwa mataimakin direkta ne na hukumar zabe mai zaman kanta INEC

Jihar Kogi - Majalisar koli na jihar Kogi ta amince da nadin Prince Mathew Alhaji Opaluwa a matsayin Attah na masarautar Igala kamar yadda The Sun ta ruwaito.

Majalisar ta bada amincewarta ne yayin taronta na 6 da aka yi a dakin taronta a gidan gwamnatin jihar da ke Lokoja a ranar Litinin.

Labari da ɗuminsa: Gwamnatin Kogi ta naɗa sabon Attah na Igala
Prince Mathew Alhaji Opaluwa. Hoto: Daily Trust
Source: Facebook

Daily Trust ta ruwaito cewa Opaluwa shine na tara cikin 16 kuma na hudu cikin 'ya'ya maza na marigayi Cif Opaluwa na gidan saurauta na Aju Ameacho a masarautar Igala.

Read also

Jami'an yan sanda 34,587 da Jirage 3 zamu tura zaben jihar Anambra, IGP Alkali

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Takaitaccen tarihin sabon basaraken

Sabon Attah da aka nada ya fara karatunsa ne a St Boniface Primary School, Idah a 1975 sannan ya yi gaba zuwa St Peter’s College, Idah inda ya samu shaidar kammala sakandare ta West African School Certificate (WASC), a 1980.

Ya hallarci makarantar sharen fage da ke Ugbokolo a jihar Benue a 1981 sannan ya tafi Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a wannan shekarar ya samu digiri a bangaren nazarin kasuwanci a 1986.

Kazalika, ya yi digiri na uku (MBA) a bangaren koyan dabarun kasuwanci a 1997.

Kafin nadinsa, ya yi aiki a hukumar zabe mai zaman kanta INEC a 1988 har ya samu karin girma ya zama mataimakin direkta.

Ya yi aiki a wurare da dama a kananan hukumomin jihar Kogi, Kaduna da babban birnin tarayya Abuja a matsayin jami'in zabe yayin da a Katsina shine ke kula da sashin bincike da adana bayanai na hukumar zaben.

Source: Legit.ng

Online view pixel