Jami'an yan sanda 34,587 da Jirage 3 zamu tura zaben jihar Anambra, IGP Alkali

Jami'an yan sanda 34,587 da Jirage 3 zamu tura zaben jihar Anambra, IGP Alkali

Hukumar yan sandan Najeriya za ta tura jaruman jami'anta kimanin 35,000 jihar Anambra gabanin zaben gwamnan jihar da zai gudana ranar 6 ga Nuwamba, 2021.

Sifeto Janar na hukumar IGP Usman Alkali Baba ya bayyana hakan yayin ganawa da kwamishanonin yan sandan jihohi da kwamandoji a Abuja, rahoton ChannelsTV.

IGP ya kara da cewa za'a tura jirage masu saukar angulu uku domin lura da abubuwan dake gudana a jihar yayin zaben.

Hakazalika za'a tura dabbobi irinsu karnuka domin lalubo masu tada zaune tsaye.

IGP Alkali ya kara da cewa hukumar yan sanda zata hada kai da sauran hukumomin tsaro da hukumar shirya zabe INEC don tabbatar da an yi zaben lumana a jihar.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Da alamu dan tsagin Aisha Buhari zai ci zaben shugabancin APC a Adamawa

Yan sanda 34,587 da Jirage 3 zamu tura zaben jihar Anambra, IGP Alkali
Jami'an yan sanda 34,587 da Jirage 3 zamu tura zaben jihar Anambra, IGP Alkali Hoto: NPF
Asali: Facebook

Asali: Legit.ng

Online view pixel