NAF ta karyata rahoton biyan 'yan bindiga N20m don kada su harbo jirgin Buhari

NAF ta karyata rahoton biyan 'yan bindiga N20m don kada su harbo jirgin Buhari

  • Rundunar sojin saman Najeriya ta karyata jita-jita da ake yada cewa, ta biya 'yan bindiga wasu makudan kudade
  • Wata jaridar kasar Amurka ta fitar da rahoton da ke cewa an ba 'yan bindiga kudi domin su mika wani makami
  • Rundunar ta ce zunzurutun karya ne, kuma labari mara asali da tushe daga majiyoyin tsaro

Abuja - Jaridar Punch ta ruwaito cewa, rundunar sojin saman Najeriya ta yi watsi da jita-jita da wasu ke yadawa a kafafen sada zumunta cewa, an biya 'yan bindiga N20m domin su mika wata bindigar harbo jirgin yaki ga gwamnati.

A yau ne aka samu rahoton da ke yawo a kafafen sada zumunta, wanda ke cewa, gwamnatin Buhari tare da sojojin saman Najeriya sun ba 'yan bindiga N20m a jihar Katsina domin su mika makamin harbo bindiga mallakarsu.

Kara karanta wannan

Zamfara: A kalla rayuka 12 sun salwanta, 'yan bindiga sun kone motar 'yan sanda

Rundunar sojin sama ta karyata jita-jitar Buhari ya biya 'yan bindiga N20m kada su kado shi a jirgi
Jami'in runfunar sojin saman Najeriya | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Jaridar Wall Street Journal ta bayyana a cikin wani rahoto a ranar Lahadi cewa NAF ta kulla yarjejeniyar ne yayin da Shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), ke shirin tafiya Katsina, jiharsa ta haihuwa.

A cikin wata sanarwa da kakakin, Air Commodore, Edward Gabkwet ya fitar, ya ce jita-jita da ake yadawa ba komai face zunzurutun karya kuma an kirkire su ne don a bata sojin sama da sunan gwamnati.

Sanarwar ta kuma yi kira ga mutanen kasa da su yi watsi da labarin wanda ta ce na bogi ne mara tushe.

Rundunar ta ce babu wani dalili da zai sa ta biya 'yan bindiga kudi a lokacin da take ci gaba da kai masu hari a jihar Katsina da wasu sassan yankin Arewa maso Yammacin Najeriya a kokarin kawar da 'yan ta'addan.

Kara karanta wannan

Gas din girki ya fi karfin talakawa: 'Yan Benue sun rungumi aiki da icce da gawayi

A bangare guda na sanarwar, NAF ta bayyana cewa, rundunar na ci gaba da samun nasara kan 'yan bindiga a yankin Arewa masi yammacin Najeriya, Nigeria Tribune ta ruwaito.

Sojojin Najeriya sun fafata da Boko Haram, an ragargaji 'yan Boko Haram da yawa

A wani labarin, Sahara Reporters ta ruwaito cewa, akalla sojojin Najeriya uku da mayakan Boko Haram 20 sun rasa rayukansu a ranar Asabar yayin da sojoji ke kokarin kwato garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

An ce maharan sun mamaye jerangiyar gidajen 777, a wajen birnin Maiduguri da misalin karfe 10:15 na daren Asabar.

Wani rahoton daban ya ce an gaggauta tura jirage masu saukar ungulu na rundunar sojin sama don hana maharan kwace yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.