NIN/BVN: Akwai Yiwuwar Bankuna Su Rufe Kudi a Akawun Miliyan 80 a Najeriya

NIN/BVN: Akwai Yiwuwar Bankuna Su Rufe Kudi a Akawun Miliyan 80 a Najeriya

  • Bankuna da asusun ajiya za su bukaci KYC daga jama’a ko kuwa a rufe masu akawun saboda rashin NIN/BVN
  • KYC shi ne tsarin da banki yake bi domin samun muhimman bayanan da ake bukata daga duk abokin huldarsa
  • CBN ya bda umarin a rufe asusun da aka samu bai da lambobin banki na BVN ko NIN ta shaidar zama ‘dan Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Asusu sama da miliyan 70 suke cikin barazana a yau a sakamakon umarnin da bankin CBN ya ba bankunan kasuwa.

Babban bankin Najeriya na CBN ya bada umarni a rufe asusun da bai da lambobin BVN da NIN daga farkon Maris na 2024.

Bankin CBN
Bankin CBN ya wajabta NIN/BVN Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Za a toshe asusu miliyan 70-85 a kan BVN/NIN

Kara karanta wannan

Kudin shigo da man fetur ya tashi, farashin lita ya zarce N1, 200 yau a Najeriya

Idan aka aiwatar da wannan umarni, rahoton Leadership ya ce akwai asusu kimanin miliyan 85 wadanda ba su cika sharudan ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da zarar an toshe akawun, abokin huldar banki bai da damar da zai cire kudi ko ta wani irin hali ko kuwa ya aika wani asusun.

Umarnin da CBN ya bada ta ofishin darektocinsa, Chibuzo Efobi da Haruna Mustapha sun wajaba alakanta asusu da BVN da NIN.

Ana bukatar NIN da BVN a kananan asusu?

Kamar yadda Legit ta fahimta, dokar ta shafi kananan asusun ajiya irinsu Opay da kuma manyan bankunan kasuwanci na kasar.

An gargadi bankuna cewa bayan bincike, za a hukunta wadanda suka sabawa umarnin CBN, don haka aka fito da hanyoyi.

Wannan ya jawo bankuna suka rika bada dama daga manhajojinsu domin masu hulda da su su gabatar da lambobin da ake nema.

Kara karanta wannan

Hanyoyi 4 na haɗa NIN, BVN da asusun banki cikin sauƙi: “Yau ce ranar karshe”

NIN/BVN: Shugaban 'yan POS ya roki CBN

Punch ta ce shugaban kungiyar masu harkar POS, Sarafadeen Fasasi, ya roki bankin CBN ya kara wa’adi domin kammala aikin KYC.

Sarafadeen Fasasi ya ce kamar yadda alkaluma suka nuna a lokacin da ake yin rajistar BVN, za a iya rufe asusu miliyan 70 a bankuna.

Mutane kimanin miliyan 104 suke da NIN a cikin mutum miliyan 200, don haka ake ganin akwai bukatar a ba bankuna karin lokaci.

Farfado da tattalin arziki

Kwanakin baya aka ji labari Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya zauna da manyan attajiran da ake ji da su domin inganta tattalin arziki.

An bude kofar shawara ga Aliko Dangote, Abdussamad Rabiu, Tony Elumelu da Segun Ajayi-Kadir ganin yadda ake cikin matsin lamba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng