An Yi Babban Rashi: Fitacciyar Mawakiyar Yabon Addini Ta Riga Mu Gidan Gaskiya

An Yi Babban Rashi: Fitacciyar Mawakiyar Yabon Addini Ta Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Shahararriyar mawakiyar addini, Bunmi Akinaanu wadda aka fi sani da Omije Ojumi ta rasu a asibitin Legas tana da shekaru 46
  • Mawakiyar ta rasu ne bayan shafe dogon lokaci tana fama da rashin lafiya da ya shafi kafarta, duk da tarin gudunmawar kudi da ta samu
  • Masoya da yan uwa mawaƙa sun shiga jimami yayin da aka fito da wasu kyawawan halayenta da yadda wakokinta suka taba Kiristoci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Masana'antar waƙoƙin addinin Kirista a Najeriya ta yi babban rashi biyo bayan rahoton rasuwar Bunmi Akinaanu, wadda aka fi sani da Omije Ojumi.

Shahararriyar mawaƙiyar addinin ta rasu tana da shekara 46 a duniya bayan fama da jinya da ta shafe kusan shekara guda tana yi.

Mawakiyar addini, Omije Ojumi ta rigamu gidan gaskiya tana da shekaru 46
Bunmi Akinaanu, mawakiyar addinin Kirista da ta rigamu gidan gaskiya ranar 12 ga Janairu. Hoto: @bunmiomijeojumi
Source: Instagram

Mawakiyar addini ta rasu a Legas

Kara karanta wannan

Neman sulhu: Ƴan bindiga sun gindaya wa gwamnatin Katsina sharudda 8 masu tsauri

Rahotanni sun nuna cewa Bunmi ta fara rashin lafiya ne tun a shekarar 2025, inda aka bayyana cewa cutar tana da alaƙa da matsalolin da suka shafi ƙafarta, in ji rahoton Tribune.

Duk da ƙoƙarin neman magani da addu'o'in da masoyanta suka yi, mawaƙiyar ba ta samu waraka ba, inda ta riga mu gidan gaskiya a ranar Lahadi, 12 ga watan Janairu, 2026, a wani asibiti da ke Legas.

Kafin rasuwarta, an samu ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta, inda babban malamin addini, Pastor Segun Arole, ya nuna damuwarsa kan rashin samun cikakkun bayanai game da lafiyarta bayan an tara kuɗaɗen taimako.

Ya rubuta a shafinsa na Instagram cewa:

"Ba za sanya mu mana mu ci gaba da addu'a ba tare da sanin halin da take ciki ba... Bai kamata a kyale wannan matar ta mutu ba."

Sanarwar rasuwar mawakiya Ojumi

Sai dai kash, kwana ɗaya bayan wannan kira, iyalanta suka fitar da sanarwar rasuwarta ta hannun abokin aikinta, Alayo Melody.

Sanarwar, wadda Olawale Akinnaanu ya sanya wa hannu, ta tabbatar da cewa Evangelist Olubunmi Akinnaanu Adeoye ta riga mu gidan gaskiya kuma iyalanta suna neman addu'o'in gare ta.

Kara karanta wannan

Sanata Barau zai fara raba kudi duk wata a Kano da kayan tallafi daban daban

Sanarwar ta ce:

"Cikin bakin ciki muke sanar da rasuwar Evanglist Olubunmi Akinnaanu Adeoye (Omije Ojumi).
"Ta rasu ne a ranar 12 ga Janairu, 2026 a wani asibiti a Legas, Najeriya.
"Ubangiji ya sa mutuwa hutu ce a gare ta."
An tabbatar da cewa makiya Omije Ojumi ta dade tana taba zukatan Kiristoci da wakokinta na bishara.
Bunmi Akinaanu, mawakiyar addinin Kirista da ta riga mu gidan gaskiya ranar 12 ga Janairu. Hoto: @bunmiomijeojumi
Source: Instagram

Rayuwar mawakiyar da ayyukanta

Bunmi Akinaanu ta fara harkar waƙa tun tana ɗan shekara 10, kuma ta bar aikin banki domin duƙufa ga hidimar Ubangiji ta hanyar waƙoƙin yabo.

Ta yi fice sosai ne da waƙarta mai suna "Omije Ojumi", waƙar da ta taba zukatan dubban Kiristoci a Najeriya kuma take zama jagora a gidaje da majami'u da dama.

Rasuwar tata ta jefa mawallafa, mawaƙa, da dukkan masoyanta cikin baƙin ciki, inda mutane da dama ke bayyana ta a matsayin jaruma wadda ta yi amfani da muryarta wajen yada sakon bishara da sanyaya zukatan masu rauni.

Hatsarin mota ya rutsa da mawakiya

A wani labari, mun ruwaito cewa, fitacciyar mawakiya kuma jarumar fina-finai, Angie Stone, ta rasu tana da shekaru 63 bayan hatsarin mota ya rutsa da ita.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda 11 sun ji ruwan azaba a hannun sojoji, sun ajiye makamansu a Borno

Hatsarin ya faru ne yayin da ita da tawagarta ke kan hanyarsu ta zuwa Atlanta bayan sun kammala gabatar da wasa a Mobile, Alabama.

An rahoto cewa mawakiya Angie Stone na shirye-shiryen gabatar da wani gagarumin abu da zai rikita Birtaniya kafin mutuwa ta dauke ta kwatsam.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com