Bidiyo: An Tsinci Gawar Jarumin Fina Finan Najeriya a Dakin Otel a Kasar Waje

Bidiyo: An Tsinci Gawar Jarumin Fina Finan Najeriya a Dakin Otel a Kasar Waje

  • Jarumin fina finan Najeriya kuma mai wasan barkwanci, Odira Nwobu ya mutu a Afirka ta Kudu yana da shekaru 43
  • Rahotanni sun ce an tsinci gawarsa a cikin dakin otel din da ya sauka, bayan ya je Afrika ta Kudu daukar tallar wani kamfani
  • An ga jarumin kwance a gado a wani bidiyo da ya yadu a soshiyal midiya, abin da ya jawo martani daga abokan sana'arsa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Afrika ta Kudu - Fitaccen jarumi, kuma mai shirya bidiyon ban dariya, Odira Nwobu, ya rasu a Afirka ta Kudu yana da shekara 43.

Lauyansa da kungiyar jaruman Najeriya (AGN) ne suka tabbatar da rasuwar Odira Nwobu, wacce ta girgiza masana'antar Nollywood.

Fitaccen jarumin Nollywood, Odira Nwobu ya rasu a Afrika ta Kudu
Jarumin fina finan Najeriya, Odira Nwobu da ya rasu. Hoto: ODIRA NWOBU
Source: Facebook

Mutuwar Nwobu ta girgiza jama'a a Najeriya, inda mutane da dama suka yi ta zubar da hawaye da mika ta’aziyyarsu a shafukan sada zumunta, in ji rahoton Premium Times.

Kara karanta wannan

Ahmad Gumi ya bada sharadin tsayawa Nnamdi Kanu a fito da shi daga kurkuku

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jarumin fina finan Najeriya ya rasu

Iyalinsa ba su fitar da wata sanarwa ba tukuna, kuma har yanzu ba a san abin da ya jawo mutuwarsa ba, kamar yadda lauyansa, Chukwujiekwu Chukwudi, ya ce ana jiran rahoton likitan binciken gawa.

A wani bidiyo da ya yadu, an nuna gawar jarumin kwance a kan gadon dakin otel din da yake ciki, wanda ya jefa masoyansa cikin kunci.

Lauyansa ya ce an same shi shi kadai a dakinsa a otel din da ke Benoni, kusa da Johannesburg, kwance ba ya motsi.

Ko da aka hanzarta kiran motar asibiti, ma'aikatan lafiyar suka yi kokarin farfaɗo da shi, amma abin ya ci tura, aka tabbatar da rasuwarsa nan take.

Rahoto ya nuna cewa an haifi jarumi Nwobu a jihar Enugu a 1982 kuma ya fara fim bayan gama sakandare a fim din Joseph the Dreamer.

Kara karanta wannan

Matakai 5 da Bola Tinubu ya dauka bayan sace dalibai a Kebbi da Neja

Shaharar jarumi Nwoba da mutuwarsa a waje

Tun daga lokacin ya fito a fina-finai fiye da 60, yawancinsu na barkwanci. A 2021 ya shaida wa BBC News Igbo cewa ya koma daukar bidiyoyinsa da kansa saboda ya gaji da yadda ake sanya shi yana taka rawa iri daya a fim.

Ya tara dubban mabiya a TikTok, Instagram da YouTube, inda ya zama daya daga cikin fitattun masu kirkirar bidiyoyin nishaɗi, in ji rahoton BBC.

Shugaban AGN, Emeka Rollas, ya ce Nwobu ya je Afirka ta Kudu ne tare da wasu sannannu domin tallata kamfanin gidaje na wani dan Najeriya.

Lauyansa, Chukwudi ya ce suna tattaunawa kan yadda za su sanar da iyalansa mutuwarsa sai kawai labarin ya yadu zuwa Najeriya.

An ce jarumi Odira Nwobu ya je Afrika ta kudu daukar wata talla, amma ya rasu a dakin otel.
Jarumin Nollywood, Odira Nwobu. Hoto: ODIRA NWOBU
Source: Instagram

Jarumai sun yi kukan mutuwar Nwobu

Abokin aikinsa, Awuzie Frankline, shi ne na farko da ya wallafa bidiyon jarumin kwance ba rai. Cikin alhini ya wallafa cewa:

“Ya Ubangiji, ODIRA me ya sa ka tafi ka bar mu da wuri haka? Wannan labari ya kashe mani zuciyata.”

Kara karanta wannan

Bayan fasa zuwa kasashen waje, ADC ta gayawa Tinubu abin da ya kamata ya yi

Daga baya ya wallafa wani bidiyo da aka dauka awanni kafin mutuwar jarumin, inda aka ga yana dariya da walwala, abin da ya kara jefa mutane a jimami.

Jaruma Evan Okoro ta rubuta:

“Na gaza yarda! Wannan labari ya yi muni sosai.”

El Bushido ya ce:

“Yanzu ya mutu? Rayuwa ba ta da tabbas.”

Har yanzu dai ana jiran sanarwa daga iyalansa, da kuma rahoton likitoci domin sanin musabbabin mutuwarsa, yayin da wasu ke zargin cewa hawan jini ne.

Kalli bidiyon jarumin da El Vida ya wallafa a shafinsa na Facebook a nan:

Jarumin fim, Baba Gebu ya rasu

A wani labarin, mun ruwaito cewa, masana'antar Nollywood ta shiga jimami bisa rasuwar fitaccen dan wasan kwaikwayo, Prince Oyewole Olowomojuore.

Jarumin, wanda aka fi sani da Baba Gebu ya mutu ne a jiya Laraba, 12 ga watan Nuwamba, 2025 bayan fama da jinyar wata cuta da ba a bayyana ba.

Jarumin Nollywood, Kunle Afod ya bayyana marigayin a matsayin gwarzo, wanda ya bar tarihin da za a jima ba a manta da shi ba a masana'antar Nollywood.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com