Bayan Rasuwarsa, An Ji Yawan Kadarorin Buhari da Tsabar Kuɗi da Ya Ajiye a Banki
- A 2015, Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa $150,000 ne kacal a bankinsa, abinda ya kara tabbatar da rayuwar sa ta zuhudu
- Buhari ya mallaki gidaje, gonaki, shanu 270, tumaki 25, da filaye, amma a lokacin da ya sauka daga mulki, an ce shanunsa sun ragu
- Mai magana da yawunsa Garba Shehu ya bayyana cewa dukiyar Buhari ba ta karu ba har zuwa lokacin da ya sauka daga mulki a 2023
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - A watan Satumbar 2015, Shugaban Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa yana da $150,000 (kimanin fam 100,000) ne kacal a asusun bankinsa.
Mai magana da yawunsa, Garba Shehu, ya ce wannan adadin ya nuna cewa tsohon shugaban mulkin soja kuma ministan man fetur ya kasance yana rayuwa ta zuhudu, watau gudun duniya.

Source: Twitter
Kadarori da kudin Buhari kafin hawa mulki
Will Ross, wakilin jaridar BBC ya ce wannan dukiya ƙaramin abu ce ga ƴan siyasar Najeriya. Sai dai, babbar arziki ce ga yawancin al'ummar ƙasar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Idan ba a manta ba, an zaɓi Buhari matsayin shugaban kasa a Maris, 2023, kuma an zabe shi saboda alƙawuran da ya dauka na magance cin hanci da rashawa da kuma rashin tsaro.
An bayyana dukkanin dukiyar da Buhari ya mallaka kamar haka:
- Gidaje biyar ginin bulo da bulo da gidajen ƙasa guda biyu, da kuma gonaki.
- Gonar ƴa'yan itatuwa da filin kiwo mai dauke da shanu 270.
- Tumaki 25, dawakai biyar da nau'ikan tsuntsaye daban-daban.
- Hannun jari a kamfanoni uku.
- Filaye biyu da ba a gina ba.
- Ya sayi motoci biyu daga kudinsa.
Dukiyar Buhari bayan barin mulki
Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya miƙa fom ɗin bayyana kadarorinsa ga hukumar da'ar ma'aikata (CCB), bisa sharadin Babi na 6 na Kundin Tsarin Mulki.

Kara karanta wannan
'Ba zan bar maku gadon dukiya ba,' Abin da Buhari ya fadawa ƴaƴansa kafin ya rasu
CCB ta fitar da takardar tabbatar da karɓar fom ɗin, kamar yadda Garba Shehu ya sanar a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X a ranar 3 ga Yuni, 2023.
Garba Shehu ya ce:
"Bayanan da ya cika sun nuna cewa ba a samu ƙaruwa a dukiyarsa ba, a gida ko wajen ƙasar, kuma bai ƙara sabon asusun banki ba sai wanda yake dashi tun farko a Union Bank, Kaduna. Bai karbi wani rance ba kuma babu bashin da ake binsa.
"Adadin dabbobin gonarsa ma ya ragu kadan saboda kyautar da ya bayar cikin shekaru hudu da suka gabata."

Source: Twitter
Ra'ayin Will Ross daga Legas
Will Ross ya lura cewa:
"An daɗe ana gaya mana cewa Muhammadu Buhari ya fi son rayuwa mai sauƙi, kuma yanzu a cewar mai magana da yawunsa akwai shaidar da ke goyan bayan hakan.
"Muhammadu Buhari ba talaka bane. An gaya mana cewa yana da ƙasa da Dala $150,000 a asusun bankinsa – dukiya ce mai yawa ga yawancin al'ummar ƙasar.
"Amma watakila daidai take da ƙaramin kuɗi ga mutane da yawa da ke aiki a duniyar siyasar Najeriya mai cike da abubuwan mamaki."
"Ba zan barwa 'ya'yana dukiya ba" - Buhari
A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taba fadawa ‘ya’yansa cewa ba zai bar musu gadon dukiya ba, illa kawai ya tabbatar sun sami ilimi da tarbiyya.
Ya bayyana hakan ne a ranar 13 ga watan Yuli, 2022, yayin wata ziyarar da ya kai garinsu Daura a lokacin yana rike da madafun iko a Najeriya.
Kafin rasuwarsa a ranar 13 ga watan Yuli, 2025, Buhari ya kuma shaida wa Sarkin Daura irin tarbiyyar da yake fatan a rika ba wa yara domin su zama nagari.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

