Sheikh Isma'il Maiduguri Ya Hadu da Baban Chinedu, Ya ba Shi Shawarar Wa'azin Musulunci

Sheikh Isma'il Maiduguri Ya Hadu da Baban Chinedu, Ya ba Shi Shawarar Wa'azin Musulunci

  • Bayan barin wasan barkwanci da fara wa’azin kare Musulunci, Baban Chinedu ya na samun goyon baya daga wasu malamai Najeriya
  • Fitaccen makarancin Kur'ani, Alaramma Isma’il Maiduguri, ya gana da Baban Chinedu a Abuja inda ya karfafa shi kan aikin da ya dauko
  • Biyo bayan bayyanan lamarin, jama’a da dama sun tofa albarkacin bakinsu a shafukan sada zumunta, ana yi masa addu’a da fatan alheri

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Bayan ya ajiye wasan barkwanci, ya rungumi wa’azin kare Musulunci, Baban Chinedu yana samun karfafa gwiwa daga malamai da al’ummar Musulmi.

Daga cikin waɗanda suka goyi bayansa har da Alaramma Isma'il Maiduguri, wanda ya gana da shi a Abuja domin karfafa shi a sabon aikin da ya dauko.

Kara karanta wannan

Rikicin sarauta: Dalung ya yi gargadi kan 'shirin' saka dokar ta baci a Kano

Baban Chinedu
An karfafi Baban Chinedu bayan fara wa'azi. Hoto: Isma'il Maiduguri|Baban Chinedu
Asali: Facebook

Alaramma Isma'il Maiduguri ya bayyana yadda ya hadu da Baban Chinedu a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jama’a da dama sun yi tsokaci a shafukan sada zumunta, suna yabawa matakin Baban Chinedu da kuma fatan Allah ya tabbatar da shi kan wannan hanya.

Isma’il Maiduguri ya gana da Baban Chinedu

A wata ganawa da suka yi a Abuja, Alaramma Isma'il Maiduguri ya karfafa Baban Chinedu tare da ba shi shawarwari kan wa’azin Musulunci.

Alaramma Isma’il Maiduguri ya bayyana cewa Allah ne ke karfafa zukatan mutane domin fahimtar Musulunci a hakikaninsa.

Ya kara da cewa Allah ya na taimakon addininsa ta hanyoyi da dama, ya na bude kirjin mutane domin su rungumi Musulunci da gaske.

Chinedu
Baban Chinedu a shigar barkwanci. Hoto: Baban Chinedu
Asali: Facebook

Jama’a sun tofa albarkacin bakinsu

Bayan Isma'il Maiduguri ya wallafa bayanin haduwarsa da Baban Chinedu, mutane da dama sun yi tsokaci kan lamarin, suna musu fatan alheri.

Kara karanta wannan

Kwamishinan Abba ya yi murabus ana tsaka da takaddamar sarautar Kano

Wani mai suna Serbia Boy ya ce:

"Na san za ka yi abu mafi girma da wannan, saboda Musulunci ya na cikin ranka, Shettima."

Habibullah Matawalle ya ce:

"Ameen ya Allah! Abin da ya kamata kungiyar Izala ta yi kenan, su same shi, su karfafe shi, su tallafa masa a wannan kyakkyawan aiki."

Fatan alheri da addu’o’in al’umma

A cikin wadanda suka yi tsokaci da addu'o'i akwai wani mai suna Abubakar Abba Kringim, wanda ya ce:

"Masha Allah! Baban Chinedu, Allah ya saka da gidan Aljanna, ya kara maka ilimi mai amfani."

Imam Shehu Liman ya ce:

"Ameen! Allah ya shiga lamuranmu, ya sa mu zama silar shiriyar mutane da yawa domin su tsira a Lahira."

Mudassir Abdulwahab Kukasheka ya ce:

"Da fatan Allah ya kara wa rayuwarka albarka, Baban Chinedu."

Jama’a da dama na ci gaba da goyon baya da addu’o’i ga Baban Chinedu, suna mai fatan Allah ya tabbatar da shi kan wannan sabon aiki da ya dauko.

Kara karanta wannan

Ali Nuhu ya sanar da rasuwar fitaccen jarumin Kannywood, Baba Karkuzu

Legit ta tattauna da Muhammad Abubakar

Wani malamin addini a jihar Taraba, Ustaz Muhammad Abubakar ya yaba da yadda Alaramma Isma'il Maiduguri ya ba Baban Chinedu shawari.

Malamin ya ce:

"Duk lokacin da wani abu sabo ya fito dama malamai ne ya kamata su kalle shi ta mahangar ilimi.
'Ya kamata a nusar da Baban Chinedu yadda ya kamata ya tafiyar da wannan aiki da ya fara domin jin tsoron kar ya kauce hanyar Musulunci."

Sheikh Asadus Sunnah ya yabi Baban Chinedu

A wani rahoton, kun ji cewa, Sheikh Musa Yusuf Asadussunnah ya yaba wa Baban Chinedu da ya fara wa'azin addinin Musulunci.

Sheikh Musa Yusuf Asadussunnah ya ce dama Allah na amfani da mutane daban daban wajen taimakon addininsa ta hanyar da ba a tsammani.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng