Sheikh Gumi Ya Rama Miyagun Maganganu da El Rufa'i Ya Fada Masa a Baya

Sheikh Gumi Ya Rama Miyagun Maganganu da El Rufa'i Ya Fada Masa a Baya

  • Sheikh Ahmad A. Gumi ya yi martani kan sauya shekar da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya yi zuwa jam’iyyar SDP
  • Malamin ya nuna El-Rufa’i ya taba yin maganganu marasa dadi kansa, shi ma zai yi amfani da damarsa wajen mayar da martani
  • Ya ce sauyin da El-Rufa’i ya samu daga mulki zuwa dan adawa wa’azi ne ga sauran shugabanni masu girman kai a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Malamin addini a Najeriya, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya yi martani mai zafi kan sauya shekar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya yi.

Malamin ya nuna cewa a baya El-Rufa’i ya yi rushe-rushe da zaluntar mutane, amma yanzu da aka kwace mulki a hannunsa sai ya dawo yana kuka.

Kara karanta wannan

Zargin El Rufai: Gwamna Uba Sani ya yi martani, ya fadi abin da ya sa a gaba

Sheikh Gumi
Sheikh Gumi ya yi martani ga El-Rufa'i. Hoto: Nasir El-Rufa'i|Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanan da Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya yi ne a cikin wani bidiyo da Anas Halliru ya wallafa a shafinsa na Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sheikh Gumi ya mayar wa El-Rufa’i da martani

Sheikh Gumi ya ce ya kamata mutane su koyi darasi daga yadda El-Rufa’i ke kokarin nuna gazawar gwamnati bayan ya sauka daga mulki.

Malamin ya yi nuni da cewa a lokacin da tsohon gwamnan ke kan mulki, bai yi la’akari da ra’ayoyin mutane ba, sai da ya rasa mukaminsa sannan ya fara sukar gwamnati.

Sheikh Gumi ya kara da cewa ya kamata irin wannan hali ya zama wa'azi ga sauran shugabanni da suke rike da karagar mulki.

"Wani mutum ya ke ba ni labari a Zariya cewa ya fadi miyagun maganganu game da ni, na ce bari in samu nima in rama."
"Ya ce ba dattijai, yanzu kuma ya na bin dattijai"

Kara karanta wannan

Madalla da hutu ga yan sakandare domin azumin watan Ramadan

'Mulkin duniya ba na har abada ba ne'

Malamin ya ce matsalar shugabanni da dama ita ce, suna girman kai idan sun samu mulki, ko kuma idan mutum ya samu kudi sai ya yi girman kai.

Sheikh Gumi ya ce:

“Ana samun mutum ya taso a cikin talakawa a kauye amma idan ya samu mulki sai ya canza abokai."

Ya bayyana cewa mutane suna canja wadanda suka taso tare da su idan suka samu wata dama wanda hakan kuma ba daidai ba ne.

Sheikh Gumi
Malamin addini a Najeriya, Sheikh Gumi. Hoto: Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi
Asali: Facebook

El-Rufa'i: Me za a fara gani a siyasar 2027?

Bayan sauya shekar El-Rufa’i zuwa SDP, ana sa ran zai kasance daya daga cikin manyan ‘yan adawa a zaben 2027.

Duk da cewa bai bayyana yin takarar shugaban kasa ba, ana ganin zai iya mara wa wani baya domin ya cimma burinsa na yaki da APC.

Hamza Al-Mustapha ya hada kai da El-Rufa'i

Kara karanta wannan

El Rufa'i ya fadi matsayarsa kan takara da Tinubu a zaben 2027

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon dogarin Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha ya sauya sheka zuwa jam'iyyar SDP.

Manjo Hamza Al-Mustpaha ya sauya sheka zuwa SDP ne domin haduwa da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i kan yaki da APC a 2027.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel