An Karrama Buhari tare da Manyan Malamai da 'Yan Siyasar Najeriya

An Karrama Buhari tare da Manyan Malamai da 'Yan Siyasar Najeriya

  • Kungiyar UFUK Dialogue ta karrama Muhammadu Buhari da lambar yabo kan kokarinsa na tabbatar da zaman lafiya a Najeriya
  • Kungiyar ta yabawa tsohon Shugaban Kasar a kan matakan da ya dauka wajen yaki da ta’addanci da karfafa tsaro yayin mulkinsa
  • Wasu fitattun mutane da suka hada da tsohon gwamnan Filato, Simon Lalong, da malaman addini suma sun samu lambar yabo

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja - Tsohon Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari, ya samu lambar yabo ta zaman lafiya daga kungiyar UFUK Dialogue.

UFUK kungiya ce mai zaman kanta da ke kokarin inganta fahimtar juna da zaman tare a cikin al’umma.

An karrama Buhari
Kungiyar UFUK ta karrama Buhari. Hoto: Mohammed Abdullahi
Asali: Facebook

Mohammed Abdullahi ya wallafa a X cewa Buhari ya yi godiya kan karrama shi da aka yi, musamman lura da cewa an ba shi lambar yabo ne bayan sauka daga mulki.

Kara karanta wannan

Rashawa: Obasanjo ya nemi kwacewa Buhari zani a kasuwa, Malami ya kare kansa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An karrama Buhari ne a wajen taron karramawa na shekara-shekara karo na takwas da kungiyar ta shirya, wanda aka hada da buda-baki.

Kungiyar ta ce karramawar na nuni da irin gudunmawar da Buhari ya bayar wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a Najeriya, musamman a lokacin da yake mulki daga 2015 zuwa 2023.

Dalilin da ya sa UFUK ta karrama Buhari

Shugaban UFUK Dialogue, Emrah Ilgen, ya ce lambar yabon da aka bai wa Buhari tana da alaka da matakan da ya dauka na yaki da ‘yan ta’addan Boko Haram da rikice-rikicen kabilanci a Najeriya.

Ilgen ya bayyana cewa Buhari ya taka rawar gani wajen karfafa tsaro, hada kai da kasashen waje don tabbatar da zaman lafiya.

Emrah Ilgen ya kara da cewa Buhari aiwatar da manufofin da suka taimaka wajen rage matsalolin tsaro a kasar.

Rahoton VON ya nuna cewa Ilgen ya ce:

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Shugaban Amurka, Trump ya samu izinin kakaba takunkumi ga Najeriya

"Lambar yabon da muke bayarwa ba wai kayan ado ba ne, alama ce ta irin ci gaban da ake iya samu idan mutane suka zabi zaman lafiya, adalci da hadin kai,"

Ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi adalci da kawo zaman lafiya a cikin al’umma, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen samar da ci gaban kasa.

Buhari
Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari. Hoto: Bashir Ahmad
Asali: Twitter

Buhari ya gode wa UFUK bisa karrama shi

An karbi lambar yabon a madadin Buhari ta hannun daya daga cikin hadimansa, Mohammed Abdullahi da 'yarsa, Nana Khadija Buhari.

Mohammed Abdullahi ya ce Buhari ya ce karramawar shaida ce ta irin sadaukarwarsa wajen tabbatar da hadin kai da cigaban Najeriya.

"Karramawa alama ce ta irin jagorancin da Buhari ya nuna wajen shawo kan matsalolin kasa da kare hadin kai,"

- Mohammed Abdullahi

Wasu fitattun mutane da aka karrama

Baya ga Muhammadu Buhari, UFUK Dialogue ta kuma karrama wasu fitattun mutane da suka bayar da gudunmawa wajen inganta zaman lafiya a Najeriya.

Kara karanta wannan

An sake rikita Tinubu, Kwankwaso, Obi da gwamnonin PDP sun shirya raba shi da mulki

Cikin wadanda suka samu lambar yabo akwai tsohon gwamnan Filato, Simon Lalong, Joseph Ochogwu, Fasto Joseph Tile Nomhwan

Haka zalika an karrama wani fitaccen malamin addinin Musulunci a jihar Neja, Malam Muhammed Nurudeen Lemu.

Kungiyar UFUK Dialogue ta ce wadannan mutane sun taka rawar gani wajen hada kan al’umma, da kokarin samar da zaman lafiya tsakanin mabambantan addinai da kabilu.

Obasanjo ya zargi Buhari da rashawa

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon ministan shari'a, Abubakar Malami ya ce ba shi da hannu wajen yin afuwa ga tsofaffin gwamnoni a zamanin Muhammadu Buhari.

Abubakar Malami ya yi bayani ne bayan Olusegun Obasanjo ya ce cin hanci da rashawa sun yi katutu a lokacin mulkin Buhari tsakanin 2015 da 2023.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel