An Karrama Tafawa Balewa a Kwara, an Sanya wa Katafaren Titi Sunan Firayim Ministan

An Karrama Tafawa Balewa a Kwara, an Sanya wa Katafaren Titi Sunan Firayim Ministan

  • Rahotanni na nuni da cewa gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq ya kammala aikin titin da ke zuwa gadar sama ta Tunde Idiagbon
  • Gwamnan ya sanya wa titin suna Tafawa Balewa domin girmama tsohon Firaministan Najeriya bisa kokari da ya yi wajen kawo cigaba a kasar nan
  • Uwargidan shugaban kasa, Oluremi Tinubu za ta kaddamar da sababbin gadojin sama biyu a Ilorin yau yayin da ta isa jihar domin ziyarar aiki

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kwara - Gwamnatin jihar Kwara ta bayyana kammala gyaran titin da ya hada gadar sama ta Janar Tunde Idiagbon a Ilorin, tare da sanya wa titin sunan Abubakar Tafawa Balewa.

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa ta sanyawa titin sunan Tafawa Balewa ne domin girmama marigayin bisa kokarin da ya yi.

Kara karanta wannan

An shiga jimami bayan tankar mai ta sake fashewa a Najeriya, mutane 11 sun rasu

Tafawa Balewa
An karrama Tafawa Balewa a jihar Kwara. Hoto: Kwara State Government
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan lamarin ne a cikin wani sako da gwamnatin jihar Kwara ta wallafa a shafinta na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan jihar, AbdulRahman AbdulRazaq, ne ya bayyana hakan a jiya yayin da ake buɗe titin ga al’ummar jihar.

AbdulRahman AbdulRazaq ya ce hakan na cikin yunkurin gwamnatin jihar na kyautatawa da samar da abubuwan more rayuwa da bunkasa tattalin arziki a Kwara.

An karrama Tafawa Balewa a Kwara

Gwamnatin Kwara ta bayyana cewa ta sanya wa titin sunan ne domin tunawa da gudunmawar da Tafawa Balewa ya bayar ga Najeriya kafin rasuwarsa a juyin mulkin soji na Janairu 1966.

Titin yana daga cikin ayyukan da gwamnatin AbdulRazaq ke yi don inganta sufuri a jihar, inda gwamnatin ta ce gyaran titin zai taimaka wajen rage cunkoso da sauƙaƙa zirga-zirga a Ilorin.

A cewar gwamnan, Tafawa Balewa mutum ne mai tarihi, kuma wajibi a tuna da irin gudunmawar da ya bayar ga Najeriya.

Kara karanta wannan

Shirin azumi: Gwamna Radda zai raba abincin Naira biliyan 9 ga talakawa a Ramadan

Masana na ganin sanya wa wannan titi sunansa wata hanya ce ta girmama shi da samar da hanyar da za a cigaba da tunawa da shi.

Remi Tinubu ta ziyarci jihar Kwara

A yau Laraba uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, za ta kaddamar da wasu muhimman ayyuka, ciki har da gadojin sama guda biyu da gwamnatin jihar ta gina.

An sanya wa gadojin sunayen Sarkin Ilorin, Dr Ibrahim Kolapo Sulu-Gambari da marigayi Janar Tunde Idiagbon.

Gadojin suna a wurare masu mahimmanci a birnin Ilorin, kuma ana sa ran za su rage cunkoson abubuwan hawa tare da inganta harkokin kasuwanci a jihar.

Karin bayani kan ziyarar Remi Tinubu a Kwara

Baya ga kaddamar da gadojin sama, Sanata Oluremi Tinubu za ta duba wasu ayyuka da gwamnatin jihar ta aiwatar, ciki har da cibiyar fasahar zamani.

Tun jiya da yamma Uwargidan Shugaban Kasa ta isa Ilorin domin ziyarar kwanaki uku da ta hada da bude ayyuka.

Kara karanta wannan

Yan sanda a Kano sun sake matsaya kan zargin ta'addanci, sun gano wani shiri a Maulidi

Gwamnatin jihar Kwara ta ce ayyukan suna daga cikin shirye-shiryen da za su kawo ci gaba mai dorewa ga jihar da ma Najeriya baki ɗaya.

An fara shirin hajjin bana a Kwara

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar alhazai a jihar Kwara ta fitar da sanarwa kan shirye shiryen hajjin bana.

Hukumar ta ce daga ranar 31 ga Janairu za a daina karbar kudin aikin hajji kuma a wata mai kamawa za a fara samar musu da biza.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

iiq_pixel