Jerin Ma'aikatun da Wuraren da aka Sanya wa Sunan Bola Tinubu bayan Hawansa Mulki
An sanyawa wasu ma'aikatun gwamnati da suka hada da cibiya, makaranta da sauransu sunanan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bayan hawansa mulkin Najeriya.
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - A makon da ya wuce aka sanya sunan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ga wani barikin sojoji a birnin tarayya Abuja.
Hakan na zuwa ne bayan sanya sunan shugaban kasar ga wasu ma'aikatun gwamnati, wanda hakan ya jawo ce-ce-ku-ce a fadin kasar nan.

Asali: Facebook
A wannan rahoton, mun tattaro muku jerin ma'aikatun gwamnatin da aka sanya wa sunan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Cibiyar BATTIC a Abuja
A watan Disambar 2024 shugaban kasa ya kaddamar da cibiyar fasahar zamani ta Bola Ahmed Tinubu (BATTIC) a Hedkwatar Hukumar Shige da Fice ta Kasa (NIS).
Cibiyar ta ƙunshi wurare huɗu na fasahar zamani da suka hada da Cibiyar Kulawa da Sarrafa Bayanan Fasinjoji da sauran wuraren cigaba.
Hukumar NIS ta wallafa a X cewa matakin wani bangare ne na kokarin gwamnati na sauya fasalin hukumomin tsaro ta hanyar amfani da sababbin fasahohin zamani.
Muhimman sassan cibiyar BATTIC
Cibiyar Fasahar Zamani ta Bola Ahmed Tinubu ta ƙunshi cibiyoyi huɗu:
i. Sashen kula da bayanan fasinjoji
Wannan cibiya ita ce ke kula da tsarin tattara bayanai da aka shigar a manyan filayen jiragen sama guda biyar na ƙasar nan.
Wannan cibiyar na da burin gano mutanen da za su iya zama barazana ga tsaron kasa da sanar da hukumomin tsaro nan take.

Asali: Facebook
ii. Sashen bayanan hukumar NIS
Wannan ita ce cibiyar da ke tattara dukkan bayanai daga ayyukan hukumar shige da fice tare da sauran jama’a.
Sashen cibiyar zai rika taimaka wa hukumar wajen tsara tsare-tsarenta da kuma daukar matakai cikin sauki.
iii. Sashen samar da katin ECOWAS
Cibiyar ta ware wajen samar da katin ECOWAS mai dauke da bayanai na zamani domin tabbatar da tsaro da hana yin katin jabu ko yin almundahana.
Hukumar ta ce wannan wani mataki ne da zai taimaka wajen karfafa tsaro a tsakanin kasashen ECOWAS.
iv. Sashen kula da iyakoki
Za a yi amfani da sababbin fasahohi kamar CCTV da na’urori masu gano motsi domin gudanar da aikin tsaron iyakoki.
Wannan sashe na da alhakin kula da duk wani motsi a iyakokin kasa da bayar da rahoto nan take idan aka samu barazana ga tsaro.
2. Kwalejin Tinubu ta kimiyya da fasaha
A ranar 21 ga Janairu aka samu rahotanni kan cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da kafa Kwalejin Fasaha ta Gwarinpa a Birnin Tarayya Abuja.
Tribune ta rahoto cewa kwalejin za ta mayar da hankali kan koyar da fasaha, sana’o’i, da kasuwanci bisa manufofin ilimin ƙasa.
Haka zalika an bayyana cewa za a sanya wa makarantar sunan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Karin bayani kan kwalejin Tinubu
Ministan ilimi, Dr Olatunji Alausa ya bayyana cewa kafa kwalejin na cikin manufofin gwamnatin shugaba Tinubu na tabbatar da cewa an bunkasa koyar da fasaha, kasuwanci, da sana’o’i.
Ya kuma bukaci Ministan Birnin Tarayya da ya ba da shawarwari kan wuraren wucin gadi da na dindindin da za a kafa kwalejin a Gwarinpa.
Bugu da kari, ya ce tawagar kwararru daga Ma’aikatar Ilimi da Hukumar Kula da Ilimin Fasaha (NBTE) za su ziyarci wuraren da aka ba da shawara domin tantance su.
3. Barikin Bola Tinubu a Abuja
A makon da ya wuce shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar da sabon barikin sojojin Najeriya a Asokoro, Abuja.
Rundunar sojin Najeriya ta wallafa a Facebook cewa an sanya wa barikin sunan Shugaba Tinubu a matsayin yabo kan goyon bayansa ga sojojin Najeriya.
Rahotanni sun nuna cewa daga cikin wuraren da aka samar akwai ofisoshi da gidajen zama, inda aka samar wa sojoji 614 matsuguni.

Asali: Facebook
Jawabin Bola Tinubu yayin taron
Da yake jawabi yayin bikin kaddamarwar, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa ginin yana nuna himmar Gwamnatin Tarayya wajen bai wa jin dadin sojoji fifiko.
Shugaban Ƙasa ya yi kira ga sojojin Najeriya da su ci gaba da kare martabar ƙasa tare da jajircewa wajen tabbatar da tsaron al’umma.
Ya kuma yaba da jajircewar shugabannin rundunar sojoji wajen ganin an aiwatar da gagarumin aikin cikin nasara.
Kalaman hafsan sojojin Najeriya
A nasa jawabin, Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya nuna godiyarsa ga Shugaban Ƙasa bisa irin goyon bayan da yake bai wa rundunar sojoji.
Ya bayyana cewa sanya wa barikin sunan Shugaba Tinubu wata alama ce ta yabawa bisa kokarinsa wajen magance matsalolin masauki da kuma karfafa rundunar.

Kara karanta wannan
Bayan kokarin titsiye shi kan badakalar $2.3bn na kwangila, Buhari ya dawo Najeriya
4. Filin jirgin Tinubu a Minna
A watan Maris na shekarar 2024 aka fara maganar sauya sunan filin jirgin saman Abubakar Imam na jihar Neja zuwa Bola Ahmed Tinubu.
A ranar 10 ga watan Maris jaridar Punch ta wallafa cewa gwamnatin tarayya ta sauya sunan filin jirgin zuwa ga sunan Bola Ahmed Tinubu.

Asali: Twitter
Abubakar Imam da aka sanya wa sunan jirgin saman a karon farko ya kasance fitaccen marubuci a Arewacin Najeriya da ya wallafa littattafai masu yawa ciki har da 'Magana Jari Ce'.
Hakan ya sanya sauya sunan jirgin zuwa Bola Tinubu ya samu suka daga Arewa sosai amma hakan ba ta canja komai ba.
PDP ta zargi Buhari kan Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta yi zargin cewa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana gazawar Bola Tinubu.
PDP ta yi magana ne bayan shugaba Buhari ya ce Allah ne kadai zai iya gyara Najeriya a wani taron masu ruwa da tsaki na APC a jihar Katsina.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng