'Rayuwar IBB': Tsohon Shugaban Najeriya Zai Fitar da Littafin da Aka Dade Ana Jira
- Ibrahim Babangida zai kaddamar da littafin tarihin rayuwarsa da aka dade ana jiran ganinsa a ranar 20 ga Fabrairu, 2025, a Abuja
- Littafin zai tabo muhimman batutuwa da suka shafi mulkinsa, ciki har da rikicin 12 ga Yuni da shirin SAP da ya jawo ce-ce-ku-ce
- Manyan shugabanni, ciki har da Shugaba Bola Tinubu da Obasanjo, za su halarci kaddamarwar tare da tara kudin gina gidan tarihi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Tsohon shugaban Najeriya, Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), ya shirya kaddamar da littafin tarihin rayuwarsa mai suna: A Journey in Service.
Ana sa ran za a kaddamar da littafin ne a ranar 20 ga Fabrairun 2025, a dakin taro na otel din Transcorp Hilton da ke Abuja.

Asali: Twitter
IBB zai fitar da littafin rayuwarsa
Wannan littafi ya zo ne bayan shekaru 32 da IBB ya bar mulki, wanda aka yi masa lakabi da "Maradona" da "hatsabibin mai fikira" inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mulkin IBB ya gamu da kalubale da tarin ce-ce-ku-ce musamman a kan wani shiri na SAP da ya bullo da shi wanda ya haifar da zanga zanga da rikicin tattalin arziki.
Wasu daga cikin abubuwan da suka jawo ka-ce-na-ce a lokacin mulkinsa sun hada da kashe Dele Giwa da kuma rushe zaben ranar 12 ga Yuni.
IBB ya ji matsin lamba ya yi murabus
IBB ya ce kafofin watsa labarai ne suka kirkiro masa lakabin “Maradona” saboda kwarewarsa wajen sarrafa siyasa.
“Suna kira ni da ‘hatsabibin mai fikira’, wannan ya ba ni mamaki, domin an gama mutum hatsabibi sannan kuma mai fikira,” inji shi.
Sai dai a watan Agustar 1993 ne IBB ya ji matsin lamba sosai daga masu adawa, inda ya yi murabus domin ba da kai bori ya hau.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Kano ta yafewa masu zanga zanga, an dakatar da shari'ar zargin cin amanar kasa
IBB ya ce ya dauki wannan matakin ne domin ya rage matsin lambar da ake yi masa, inda ya mika mulki ga marigayi Ernest Shonekan.
Duk da cewa ya yi hira da kafofin watsa labarai, akwai muhimman batutuwa da ya dade bai yi bayani kai tsaye a kai ba.
IBB ya canja shawara kan rubuta tarihinsa
Shekaru bakwai da suka wuce, IBB ya nuna shakku kan rubuta tarihin rayuwarsa, yana mai cewa mutane ba za su so karantawa ba.
Ya bayyana cewa an samu kuskuren fahimta game da wasu abubuwan da suka faru a mulkinsa daga shekarar 1985 zuwa 1993.
Duk da haka, ya canja shawara kuma ya rubuta littafin, wanda zai kunshi tarihin rayuwarsa da muhimman labarai game da mulkinsa.
Tinubu zai jagoranci kaddamar da littafin IBB
Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai jagoranci taron kaddamarwar tare da tsofaffin shugabannin Najeriya da na wasu kasashen Afrika.
An gayyaci Olusegun Obasanjo ya jagoranci taron yayin da Shugaba Tinubu zai kasance babban bako na musamman.
Tsohon shugaban Ghana, Nana Akufo-Addo, zai gabatar da jawabi, sannan Yemi Osinbajo zai yi bitar littafin.
Za a gina gidan adana tarihin rayuwar IBB
Tsofaffin shugabanni da suka hada da Muhammadu Buhari, Yakubu Gowon, Abdulsalami Abubakar, da Goodluck Jonathan za su halarci taron.
Ana kuma sa ran tsohon ministan tsaro, Theophilus Danjuma, da shugaban BUA Group, Abdul Samad Rabiu, za su zama jagororin kaddamarwar.
Taron zai gudana tare da tara kudaden gina gidan adana tarihin rayuwar IBB mai suna IBB Presidential Library.
Wannan littafi zai bada damar ganin tarihin siyasa da abubuwan da suka wakana a lokacin mulkinsa a kasar Najeriya.
Muhimman abubuwa game da IBB
Tun da fari, Legit Hausa ta rahoto wasu muhimman abubuwan sani game da tsohon shugaban Najeriya na mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida (IBB).
Mun yi bayani game da rayuwar IBB wanda tarihin Najeriya ba zai cika ba sai da shi ne a lokacin da ya cika shekaru 83 da haihuwa a ranar 17 ga watan Agustan 2024.
Asali: Legit.ng