El Rufai, Shetty da Mutane 17 da Tinubu Ya ba Mukamai Amma daga baya Ya Soke Nadin
- Shugaba Bola Tinubu ya yi nade naden mukamai, amma daga baya ya soke su, abin da ya jawo ce-ce-ku-ce a cikin al'ummar kasar
- Anamayi Dorcas ta ce soke nadin mukami na iya shafar lafiyar kwakwalwa mutumin da aka sanya wa ran samun mukamin da farko
- Legit Hausa ta jero mutane 10 da Tinubu ya ba mukamai amma daga baya ya soke nadin, ciki har da Maryam Shetty, Nasir El-Rufai
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi nade-nade da dama tun bayan hawansa mulki a watan Mayun shekarar 2023.
Sai dai kuma, shugaban kasar ya sha soke nade naden da ya yi bayan sanar da nadin a fili, lamarin da ya jawo 'yan kasar suka fada diga ayar tambaya.
Mutane da dama na ganin bai kamata a ce hakan tana faruwa ba, domin akwai ka’idojin nade-nade da aka fayyace gwamnati na bi a cewar rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani tsohon minista a gwamnatin Umaru Yar’Adua, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya bayyana yadda ake nade-naden da ke bukatar sahalewar shugaban kasa.
Yadda ake tantance wadanda za a ba mukamai
Ya ce ana fara duba cancanta, kwarewa, tarihin aiki da kuma la’akari da daidaito na yankuna da addinai kafin a zabi wanda za a ba mukami.
Daga nan sai a mika sunan mutumin ga hukumomin tsaro don bincike domin tabbatar da cewa ba shi da wata alaka da aikata laifi.
Bayan samun amincewar tsaro, ana iya gayyatar mutumin ya gana da shugaban kasa, shugaban ma’aikata, ko wanda shugaban ya wakilta kafin sanarwa.
Abin da ke biyo bayan tantance mutane
Tsohon ministan ya ce a yanzu ta kai ga ana duba rubuce-rubucen mutum a shafukan sada zumunta don sanin ra’ayinsa kan gwamnati.
Wani ma’aikacin fadar shugaban kasa ya tabbatar da cewa akwai abubuwa masu yawa da ake la’akari da su wajen nada mukami.
Weekend Trust ta gano cewa idan aka sanar da sunan mutum, to yana nuna cewa an kammala dukkannin bincike kuma an cika ka’idoji na nadinsa.
Tinubu na soke nadin mutum bayan tantancewa
Amma a karkashin gwamnatin Tinubu, ko bayan an fitar da sunayen wadanda za a ba mukamai, ana iya soke nadin mutum, wasu lokuta ma ko da kuwa ya kama aiki.
Wannan yanayi ya sa mutane suka fara kaffa-kaffa wajen taya wadanda aka sanar za a ba murna, don gudun kunyar soke nadin nasu daga baya.
Soke nadin mutum bayan sanar da nadinsa ya zama ruwan dare a gwamnatin Tinubu wanda har ya haifar da shakku game da gaskiyar nade-naden da ake sanarwa.
Mutane 10 da Tinubu ya soke nadin mukamansu
Legit Hausa ta tattaro jerin mutane 10 da Tinubu ya nada mukamai, amma daga bisani ya soke nadinsu.
1. Maryam Shetty
Abin kunya mafi girma daga cikin ire-iren soke nade-naden da aka yi shi ne batun Maryam Shettima Ibrahim, wacce aka nada so nadawa minista daga Kano.
Sunan Maryam Shetty ya shiga jerin wadanda za a tantance a majalisar dattawa, kuma hakan ya zama abin magana a bainar jama’a.
Ta shirya don tantancewa kamar sauran wadanda aka nada, har ta isa ginin majalisar dattawa a ranar tantancewa tana jiran a kira ta.
Amma sai aka shaida mata cewa an janye sunanta daga jerin wadanda za a tantance.
2. Stella Okotete
Bayan tantance ministoci da jiran tabbatar da su, shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya yi wani bayani da ya ba mutane mamaki.
Akpabio ya sanar da cewa majalisar dattawa ta dakatar da tabbatar da ministoci uku saboda tana jiran izinin tsaro daga hukumomin da suka dace.
Stella Oketete, daraktar ci gaban kasuwanci a Bankin NEXIM, tana cikin ministocin da aka dakatar da tabbatar da su.
3. Nasir El-Rufai
Na biyu daga cikin ministoci uku da aka dakatar da tabbatar da su shi ne tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai.
El-Rufai ya fara nuna rashin sha’awar mukamin minista, yana cewa ya riga ya yi irin wannan aiki shekaru 20 da suka gabata.
Duk da haka, ya amince da karbar mukamin ministan bayan Tinubu ya fito a fili ya nuna cewa zai yi aiki da shi kuma har El-Rufai ya mika kansa domin tantancewa.
El-Rufai ya kasance cikin jiran tabbatar da shi a matsayin minista amma ya samu labarin cewa an fasa ba shi mukamin.
4. Sani Danladi Abubakar
Na uku cikin wadanda suka fuskanci irin wannan matsala shi ne Sanata Danladi Abubakar daga jihar Taraba.
An rahoto cewa an janye sunansa ne saboda kotun koli ta hana shi rike mukamin gwamnati har na tsawon shekaru 10.
Sai dai Sanata Danladi ya musanta hakan yayin da yake amsa tambayoyi daga sanatoci a lokacin tantancewar da majalisar dattawa ta yi masa.
Duk da ya kare kansa yayin tantancewar, ba a tabbatar da nadinsa ba.
5. Imam Ibrahim Kashim
Haka zalika akwai batun Imam Ibrahim Kashim, wanda aka nada a matsayin shugaban Hukumar Gyaran Hanyoyi ta Kasa (FERMA).
An samu cece-kuce sosai bayan sanar da nadin Imam, saboda duka duka shekarunsa 24. Ana ganin ya yi matukar kankanta da rashin kwarewa da mukamin.
Gwamnati ta mika wuya ga matsin lambar jama'a, inda ta soke nadin cikin kasa da mako daya bayan sanarwar, inji rahoton BBC.
6. Rikici a CCT kan shugabancin Umar da Kogo
Haka zalika rikici ya kunno kai a Kotun Ladabtar da Ma’aikata (CCT) inda Danladi Umar da sabon shugaba, Mainasara Kogo, ke ikirarin shugabanci.
Umar ne ya ke jagoranci kotun, amma aka cire shi ta hanyar kudurin majalisar dokoki ta kasa.
Shugaba Tinubu ya nada Kogo a matsayin sabon shugaban CCT a ranar 13 ga Yuli, amma aka samu matsala a hanyar da aka bi wajen cire Umar.
Lamarin dai ya yi tsamari har da zuwa kotu, wanda hakan ya sa har yanzu Umar ke ikirarin cewan shi ne shugaban kotun CCT.
7. Janye nadin Danfulani a SMDF
Shugaba Tinubu ya nada Yazid Shehu Umar Danfulani a matsayin sakataren zartarwa na Hukumar Ci gaban Harkokin Ma'adinai (SMDF/PAGMI)
An ce wannan ya dogara ne da tsammanin cewa lokacin Fatima Shinkafi a matsayin sakataren zartarwa ya kare.
Fatima Shinkafi ta dage cewa lokacin ta bai kare ba, kuma gwamnati ta sauya shawara a kan wannan inda Tinubu ya soke nadin da aka yi wa Yazid.
8. Shugaba da mambobin SEDC
A wannan watan ne, aka soke nadin Hon. Emeka Atuma, wanda aka sanar da shi a matsayin shugaban hukumar ci gaban Kudu maso Gabas (SEDC), tare da maye gurbinsa da Dr. Emeka Nworgu.
Dukkanin daraktocin zartarwa uku da aka nada a farko, an maye gurbinsu, sannan an nada sabbin daraktocin zartarwa guda biyu.
Shugaban kasa ya kuma cire daya daga cikin mambobin hukumar, Donatus Eyinnah Nwankpa, sannan ya maye gurbin daraktan zartarwa na kudi, Anthony Ugbo, da Stanley Ohajuruka.
9. Shugaba da mambobin NWDC
Shugaban kasa ya sauya shugabannin farko na Hukumar ci gaban Arewa Maso Yamma (NWDC) tare da sauya su gaba daya 'yan kwanaki da nada su.
A cikin jerin wadanda aka turawa Majalisar Dattijai a karshen Satumba domin nada su akwai Haruna Ginsau a matsayin shugaba, tare da Sanata Tijani Yahaya Kaura da Hon. Abdulkadir S. Usman a matsayin mambobi.
An maye gurbinsu da Alh. Lawal Samai’la Abdullahi a matsayin sabon shugaba, tare da Ja’afar Abubakar Sadeeq da Yahaya Aminu Abdulhadi a matsayin mambobi.
10. Tawagar Watsa Labarai
Wani lamari da ya kara jawo ce-ce-ku-ce shi ne sauye sauyen da Tinubu ya yi a tawagar watsa labarai da sadarwar shugaban kasa.
Tsohon mai magana da yawun shugaban kasa, Ajuri Ngelale, ya ajiye mukaminsa a Satumba, sannan a Nuwamba, aka nada Daniel Bwala.
Bwala ya dauka cewa an nada shi domin maye gurbin Ngelale, kuma ya fara aiki da wannan ra'ayi, amma bayan bayyana hakan ga jama'a, Tinubu ya gaggauta yin gyara.
A gyaran da Tinubu ya yi, an canja nadin Sunday Dare, daga mai ba da shawara kan sadarwar jama'a da wayar da kai zuwa mai ba da shawara kan watsa labarai.
Shi kuwa Mista Daniel Bwala, an canza mashi matsayi zuwa mai ba da shawara a bangaren watsa labarai kan tsare-tsaren gwamnati.
'Janye nadi na iya shafar kwakwalwa' - Likita
Anamayi Dorcas, likitar kwakwalwa a asibitin koyar da kimiyya na jami'ar Jos, ta bayyana cewa soke mukaman da Tinubu ke yi na iya taba lafiyar kwakwalwar mutane.
A wata hira da aka yi da Dakta Dorcas ta ce:
“Sanya wa mutum rai kan wani abu, ba wai mukami kawai ba, na iya shafar lafiyar kwakwalwa, musamman ga wanda bai taba rike irin wannan matsayin ba.”
Ta kara da cewa, idan aka janye nadin to hakan na shafar abubuwa da dama game da mutum ciki har da tunani, rayuwa da kuma canja mu'amalarsa da mutane.
Tinubu ya nada mukamai kusan 100
A wani labarin, mun ruwaito cewa Bola Tinubu ya yi rabon mukamai kusan 100 a makon da ya gabata, inda aka zakulo mutane daga jihohi 36 da Abuja.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da nada sababbin shugabannin hukumomin raya tafkin ruwa 12 da ake da su a shiyyoyi daban daban na kasa.
Asali: Legit.ng